COVID-19: Abinda yasa ake samun yawaitan mace-mace a Najeriya - FG

COVID-19: Abinda yasa ake samun yawaitan mace-mace a Najeriya - FG

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce tana fargabar akwai yiwuwar samun karuwar mace mace a kasar da ba su da alaka da coronavirus (COVID-19) tun bullar annobar a kasar.

Ta ce mafi yawancin mace macen suna faruwa ne saboda tsoro da wasu yan Najeriya ke yi na zuwa asibitoci inda za su samu kulawar da ta dace amma su ke kin zuwa don kada a gano suna da korona.

Ana kuma ganin cewa wasu daga cikin maaikatan lafiya suna kyashin duba marasa lafiya saboda tsoron kamuwa da cutar ta korona kamar yadda The Nation ta ruwaito.

COVID-19: Dalilin da yasa ake samu yawaitan mace-mace a Najeriya - FG
COVID-19: Dalilin da yasa ake samu yawaitan mace-mace a Najeriya - FG. Hoto daga The Nation
Asali: UGC

Ministan Lafiya, Osagie Ehanire da ya bayyana hakan a yayin jawabin kwamitin kar ta kwana ta shugaban kasa kan COVID-19 a ranar Jumaa a Abuja ya ce adadin wadanda suke zuwa asibiti don awo, rigakafi da haihuwa duk sun ragu.

DUBA WANNAN: Zamfara: An zartar da hukuncin kisa a kan mutumin da ya kashe mahaifiyarsa da yan uwansa mata biyu

Ya ce, "Alkalluma sun nuna cewa adadin marasa lafiya da ke zuwa asibitoci sun ragu saboda tsoron COVID-19.

"Saboda haka, muna ganin wasu mace macen da suka faru ba su da alaka da coronavirus.

"Idan mutum ya ki zuwa asibiti ya samu taimako saboda tsoron coronavirus ko kuma likitoci suka ki duba marasa lafiya.

"Alkalluma na baya bayan nan daga Cibiyar Kula da Lafiya ta Kasa (NHMIS) ya nuna cewa adadin wadanda ke zuwa asibiti ganin likita sun ragu daga miliyan 4 zuwa kimanin mililyan biyu.

"Mata masu ciki sun ragu daga miliyan 1.3 zuwa 655,000; masu haihuwa a asibiti daga 158,374 zuwa kasa da 99,000 yayin da masu zuwa rigakafi sun ragu da rabi."

Ya cigaba da cewa yana fatan idan an sassauta dokar hana fita wasu daga cikin wadannan kallubalen za su gushe, amma hakan ya danganta da yadda mutane ke kiyayye dokoki da shawarwarin hukuma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel