Kano: Akwai yuwuwar hauhawar yawan masu korona babu dadewa- Ganduje

Kano: Akwai yuwuwar hauhawar yawan masu korona babu dadewa- Ganduje

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya ce akwai yuwuwar hauhawar yawan masu cutar coronavirus a jihar Kano bayan samar da karin dakunan gwajin cutar a jihar.

Ganduje ya sanar da hakan ga manema labarai a yayin ganawa da kwamitin dakile yaduwar cutar coronavirus na Kano a ranar Juma'a, jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Ya ce an kammala shirin samar da dakunan gwaji a kananan hukumomi 36 da ke da nisa da birnin Kano.

"Za mu bude cibiyoyin gwaji a dukkan kananan hukumomi 36 da ke da nisa da birni. Za mu ci gaba da shiri, dole ne mu dauka matakan gaggawa.

"Za mu tabbatar da cewa da cewa dukkan ma'aikatun jihar nan na shirye koda irin wannan halin ko-ta-kwana ya taso," yace.

Ya kara da cewa za su kara kokari wajen tabbatar da an fatattaki annobar kwata-kwata.

Ganduje yace mulkin sa zai ci gaba da wayar wa jama'ar jihar Kano kai tare da sauran tsare-tsaren yaki da annobar.

Kano: Akwai yuwuwar hauhawar yawan masu korona babu dadewa- Ganduje
Kano: Akwai yuwuwar hauhawar yawan masu korona babu dadewa- Ganduje. Hoto daga The Cable
Asali: UGC

KU KARANTA: Ta fallasu: Kun san jikakkiyar da ke tsakanin Ganduje da El-Rufai?

Ya yi kira ga ma'aikatan lafiya da su mayar da hankali wajen kula da sauran mutane masu cutukan da ba korona ba.

Ya jaddada cewa gwamnatinsa ta horar da daruruwan ma'aikatan lafiya don yakar annobar.

Hakazalika, shugaban kwamitin yaki da cutar korona na jihar Kano, Nasir Gawuna, wanda shine mataimakin Gwamnan jihar Kano ya tunatar da jama'ar da suka kamu da cutar cewa ba karshen rayuwarsu bace ta zo.

Ya kara da kira ga wadanda basu dauke da cutar su kiyaye dokokin masana kiwon lafiya a kan kamuwa da cutar.

A wani labari na daban, a ranar Juma'a ne ministan lafiya, Osagie Ehanire ya ce an samu sauki a jihar Kano tare da daidaituwa bayan hadin guiwar wakilan gwamnatin tarayya da kwamitin yaki da cutar korona na jihar Kano.

Ehanire ya sanar da hakan ne a yayin jawabi ga kwamitin yaki da cutar korona na fadar shugaban kasa a Abuja.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel