Korona: 'Yan kasuwan Kano sun koma sayar da kayayyaki a unguwanni saboda dokar kulle

Korona: 'Yan kasuwan Kano sun koma sayar da kayayyaki a unguwanni saboda dokar kulle

'Yan kasuwa a jihar Kano sun bullo da sabuwar hanyar sayar da hajojinsu duk da dokar kulle da Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar ya saka domin dakile yaduwar annobar COVID-19.

Yan kasuwan, galibsu daga kasuwar Kantin Kwari da Kofar Wambai sun koma unguwanni a Fagge inda suka baje kolinsu kuma babu bayar da tazara tsakaninsu.

A ranar 2 ga watan Mayu ne Gwamna Ganduje ya sassauta dokar kullen inda ya bawa wasu kasuwanni ikon buduwa a ranakun Litinin da Alhamis don mutane su saya kayan azumi.

Korona: 'Yan kasuwan Kano sun koma sayar da kayayyaki a unguwanni saboda dokar kulle

Korona: 'Yan kasuwan Kano sun koma sayar da kayayyaki a unguwanni saboda dokar kulle. Hoto daga Premium Times
Source: UGC

Gwamnan ya ce za a rika zirga zirga ne daga karfe 10 na safe zuwa karfe 4 na yamma a ranakun walwalar kuma masu sayar da nama da masu sayar da kayan gwari aka bawa damar bude shaguna.

DUBA WANNAN: Zamfara: An zartar da hukuncin kisa a kan mutumin da ya kashe mahaifiyarsa da yan uwansa mata biyu

An kuma wajabta wa mutane saka takunkumin rufe fuska in ji gwamnan, kana ya shawarci mutane su rika bada tazara tsakanin su da kiyayye tsafta.

Sai dai a ranar Alhami, yan kasuwa daga Kantin Kwari da Kofar Wambai sunyi tururuwa zuwa unguwar Fagge inda suka baje kolinsu duk da dokar kullen da gwamnan ya saka.

Korona: 'Yan kasuwan Kano sun koma sayar da kayayyaki a unguwanni saboda dokar kulle

Korona: 'Yan kasuwan Kano sun koma sayar da kayayyaki a unguwanni saboda dokar kulle. Hoto daga Premium Times
Source: UGC

Wani dan kasuwa mai suna Nafiu Ubale ya shaidawa Premium Times cewa yana bukatar samun kudi domin kula da iyalansa da kuma shirin bikin sallah.

Ubale ya ce, "An rufe Kantin Kwari na tsawon watanni saboda haka mutane suna fama da yunwa.

"Ba mu da wata zabi, shi yasa muka koma nan. Muna fatan ba za mu yada cuta ba don idan ka lura muna saka takunkumin fuska."

Wani dan kasuwan da ya ce sunansa Nura ya ce, "Na san cewa bamu cikin wadanda aka sassauta wa dokar kullen amma ba ni da wata zabi ya zama dole in fito in nema wa iyalai na abinda za su ci.

"A Fagge za mu iya kasuwanci saboda kusancinsa da Kantin Kwari."

Sai dai wani magidanci a unguwar, Abdullahi Kausi ya yi kira ga gwamnatin jihar ta hana cin kasuwar da ake yi a unguwar domin hana yaduwar cutar ta COVID-19.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel