Izgilin mutuwar Kyari: Sautin muryar tsohon kwamishinan Ganduje yana nadama

Izgilin mutuwar Kyari: Sautin muryar tsohon kwamishinan Ganduje yana nadama

Tsohon kwamishinan Ganduje, Mu'azu Magaji ya nuna nadamarsa tare da darussan da ya koya bayan kwanciyarsa jinya.

BBC Hausa ta samu zantawa da tsohon kwamishinan ayyukan da ababen more rayuwa na jihar Kano.

Kamar yadda aka ji a sautin muryar tsohon kwamishinan Gandujen, ya mika godiya ga Allah da ya fito da shi daga matsanancin halin da ya fara shiga.

Ya bayyana cewa, akwai lokacin da hatta iskar shaka sai an tallafa masa da ita.

A tattaunawar, ya ce ba sau daya ba aka mutu sakamakon cutar a gabansa bayan isarsa cibiyar killacewar a dalilin harbuwa da yayi da muguwar cutar korona.

Idan za mu tuna, a cikin watan Afirilu ne shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa ya rasu sakamakon annobar korona.

Amma kuma babban abun mamaki shine yadda Injiniya Muazu Magaji ya fito tare da yin wata wallafa a shafinsa na Facebook da ke nuna murnarsa a mutuwar, lamarin da ya jawo cece-kuce.

A ranar da ya yi wannan wallafar, wacce ita ce ranar da aka birne marigayin shugaban fadar shugaban kasar, Ganduje ya sallamesa daga aikinsa.

KU KARANTA: Ta fallasu: Kun san jikakkiyar da ke tsakanin Ganduje da El-Rufai?

A wani labari na daban, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya kwatanta Almajirai da dandalin cutar coronavirus saboda rashin tsafta, wurin zama da kuma rashin kula da kai.

Saboda suna zama wurin cunkoso, basu da takamaiman wurin bacci, ba su samun abincin da ya dace kuma babu tsafta, shiyasa suka fi kamuwa, gwamnan yace kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

A saboda haka, Ganduje ya yanke hukuncin mayar da hankali wajen kafa kungiyar taimakon gaggawa don dubawa tare da bada kariya garesu saboda annobar nan.

Kamar yadda gwamnan ya bayyana, wadanda aka samu basu dauke da cutar, za a mika su ga iyayensu yayin da za a tsare wadanda ke da ita har sai sun warke. Bayan samun warakar, za a mayar da su jihohinsu tare da shaidar NCDC.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel