COVID-19: Gwamnatin tarayya ta bayyana halin da Kano ke ciki

COVID-19: Gwamnatin tarayya ta bayyana halin da Kano ke ciki

A ranar Juma'a ne ministan lafiya, Osagie Ehanire ya ce an samu sauki a jihar Kano tare da daidaituwa bayan hadin guiwar wakilan gwamnatin tarayya da kwamitin yaki da cutar korona na jihar Kano.

Ehanire ya sanar da hakan ne a yayin jawabi ga kwamitin yaki da cutar korona na fadar shugaban kasa a Abuja.

Ya ce, "Daga cikin nasarorin da muka samu a jihar Kano shine karuwar yawan wadanda ake wa gwaji. Ana gwada a kalla mutum 350 a rana daya."

Ya ce gwamnatin jihar Kano na matukar kokari wajen bude sabbin cibiyoyin killacewa a jihar, jaridar Premium Times ta ruwaito.

Ya ce kwamitin yaki da cutar na jihar Kano zai horar da manema labarai a ranar Asabar, don tabbatar da 'yan jaridar na sako rahotanni a kan cutar yadda ya dace.

Ya ce horarwar za ta matukar taimakawa wajen wayar da kan 'yan jaridun a kan hanyoyin kariya daga cutar.

Ehanire ya jinjinawa Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano wajen bada tallafin da ya dace ga wakilan gwamnatin tarayya wurin sauke nauyinsu.

Ministan ya ce kungiyar wakilan gwamnatin tarayyar sun shirya don garzaya jihohin Sokoto da Borno don taimaka wa cibiyoyinsu wajen shawo kan yaduwar muguwar cutar.

COVID-19: Gwamnatin tarayya ta bayyana halin da Kano ke ciki
COVID-19: Gwamnatin tarayya ta bayyana halin da Kano ke ciki. Hoto daga The Cable
Asali: Twitter

KU KARANTA: Ta fallasu: Kun san jikakkiyar da ke tsakanin Ganduje da El-Rufai?

A wani labari na daban, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya kwatanta Almajirai da dandalin cutar coronavirus saboda rashin tsafta, wurin zama da kuma rashin kula da kai.

Saboda suna zama wurin cunkoso, basu da takamaiman wurin bacci, ba su samun abincin da ya dace kuma babu tsafta, shiyasa suka fi kamuwa, gwamnan yace kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

A saboda haka, Ganduje ya yanke hukuncin mayar da hankali wajen kafa kungiyar taimakon gaggawa don dubawa tare da bada kariya garesu saboda annobar nan.

Kamar yadda gwamnan ya bayyana, wadanda aka samu basu dauke da cutar, za a mika su ga iyayensu yayin da za a tsare wadanda ke da ita har sai sun warke. Bayan samun warakar, za a mayar da su jihohinsu tare da shaidar NCDC.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel