COVID-19: Mutum 288 sun karu a Najeriya, Kaduna, Katsina da Jigawa sun biyo bayan Legas

COVID-19: Mutum 288 sun karu a Najeriya, Kaduna, Katsina da Jigawa sun biyo bayan Legas

Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa a Kasa (NCDC) ta ce annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 288 a fadin Najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da NCDC ta fitar da misalin karfe 11.47 na daren ranar Jumaa, 15 ga watan Mayun na shekarar 2020.

A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa karin sabbin mutum 288 da suka fito daga jihohin Najeriya kamar haka;

179-Lagos

20-Kaduna

15-Katsina

15-Jigawa

13-Borno

11-Ogun

8-Kano

DUBA WANNAN: Yadda wani mutum ya kashe dan uwansa saboda mangwaro (Hoto)

7-FCT

4-Niger

4-Ekiti

3-Oyo

3-Delta

3-Bauchi

2-Kwara

1-Edo

Har wa yau, alkalluman da hukumar ta NCDC ta fitar a ranar 16 ga watan Mayu ya nuna cewa jimillar wadanda suka kamu ta cutar ta korona a kasar 5445.

An sallami mutum 1320 bayan an tabbatar da sun warke sarai, a yayin da cutar ta hallaka jimillar mutane 171.

A wani labarin, wata babbar kotu a jihar Zamfara ta zartar da hukuncin kisa ta hanyar rataya a kan wani mutum da ya kashe mahaifiyarsa da yan uwansa mata biyu.

An gurfanar da Kamal Yusuf da wasu mutane biyu —Armayau Shehu da Caleb Humphrey a gaban kotu bisa zarginsu da aikata laifuka uku amma Humphrey ya mutu a gidan yari kafin a kammala sharia.

Laifukan da ake tuhumarsu da aikatawa sun hada da hadin baki, fashi da makami da kisa kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Da ya ke zartar da hukuncin, babban alkalin jihar, Mai sharia Kulu Aliyu ta yanke wa Kamal Yusuf hukuncin kisa ta hanyar rayata yayin da shi kuma mutum na biyu da ake tuhuma, Armayau Shehu an wanke shi an kuma sake shi.

Wanda aka yanke wa hukuncin yana da ikon daukaka kara a cikin kwanaki 90.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel