Ku taimaka ku dinga duba sauran marasa lafiya – Ganduje ya yi ma likitoci magiya

Ku taimaka ku dinga duba sauran marasa lafiya – Ganduje ya yi ma likitoci magiya

Gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya roki likitoci da jami’an kiwon lafiya na jahar su taimaka su dinga duba sauran mutane marasa lafiya, ba lallai sai masu COVID19 ba.

Gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Juma’a yayin taron bayar da horo karo na biyu ga jami’an kiwon lafiya a kan kare yaduwar cututtuka da dakile ta da aka yi a Tahir Guest Palace.

KU KARANTA: Gwamnan jahar Zamfara ya yi wasu muhimman nade nade guda 4 a gwamnatinsa

A cewar Ganduje rashin kulawar da jami’an kiwon lafiya basu baiwa sauran marasa lafiya ne ya sa ake samun mace mace a jahar, amma yin hakan zai rage mace macen.

Ku taimaka ku dinga duba sauran marasa lafiya – Ganduje ya yi ma likitoci magiya

Ganduje Hoto:Salihu Tanko Yakasai
Source: Facebook

“Ya kamata a dinga kulawa da mata da kananan yara, a dinga kula da sauran cututtukan, idan ba haka ba yakin da muke yi da COVID19 zai zama na banza, don haka nake rokonku ku kula da sauran marasa lafiya don aikinmu ya tafi bai daya.” Inji shi.

Gwamnan ya yaba da taron bayar da horon, inda ya bayyana shi a matsayin wanda ya zo a kan gaba, domin kuwa zai baiwa jahar daman kasancewa cikin shirin yakin da bullar cututtuka.

A jawabinsa, mashiryin taron, Farfesa Bola Yinka ta ce mutane 350 da suka horas an zabo su ne daga cikin likitoci, jami’an jinya da jami’an gwaje gwaje daga asibitoci 42 a jahar.

Bola ta ce ma’aikatan za su samu horo ne a kan yadda za’a kauce ma cututtuka masu yaduwa tare da dakile yaduwarsu, da kuma dabarun kare kai a yayin da suke gudanar da aikinsu.

Daga karshe Bola ta ce suna sa ran ma’aikatan za su horas da sauran ma’aikatan da suke aiki tare dasu idan sun koma asibitocinsu.

A wani labari kuma, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana farin cikinsa da samun labarin lafiyar da mai martaba Sarkin Daura, Alhaji Farouk Umar Farouk yake samu.

Gidan talabijin na Channels na ta ruwaito baya ga farin cikin da Buhari ya nuna game da lafiyar Sarki, shugaban ya jinjina ma ma’aikatan kiwon lafiyan da suka kula da Sarkin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel