Gwamna Zulum ya bada umarnin biyan albashin ma’aikata da fansho saboda karamar Sallah

Gwamna Zulum ya bada umarnin biyan albashin ma’aikata da fansho saboda karamar Sallah

Gwamnan jahar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya bayar da umarni a biya ma’aikatan jahar albashin watan Mayu da kudin yan fansho saboda hidimar Sallah.

Jaridar The Cables ta ruwaito shugaban kungiyar kwadago ta jahar Borno, Bulama Abiso ne ya bayyana haka a ranar Juma’a, 15 ga watan Mayu.

KU KARANTA: Gwamnan jahar Zamfara ya yi wasu muhimman nade nade guda 4 a gwamnatinsa

Cikin sanarwar da ya aika ma ma’aikata, Abis yace duk da dai rabin watan kawai aka ci, amma gwamnan ya bada izinin biyan kudaden don a taimaka ma ma’aikata su fara hidimar sallah.

Gwamna Zulum ya bada umarnin biyan albashin ma’aikata da fansho saboda karamar Sallah

Gwamna Zulum Hoto: Daily Nigerian
Source: UGC

“Kungiyar kwadago ta jahar Borno na farin ciki da yadda Gwamna Zulum ke biyan albashin ma’aikata ba tare da bata lokaci ba, da kuma kudaden yan fasho da sauran hakkokinsu.

“NLC na farin ciki da yadda gwamnan ya biya albashin watan Disamba kafin bikin kirsimeti, da na watan Afrilu tun kafin a fara azumin Ramadana, yanzu kuma ya biya albashin Mayu kafin Sallah.

“Duka wannan na nuni da matsayin ma’aikata a wajen gwamnan, kuma don haka kungiyar kwadago take kira ga ma’aikata su jajirce wajen gudanar da aikinsu domin amfanin jama’an jahar.” Inji shi.

A wani labari kuma, Gwamnan jahar Zamfara, Bello Matawalle ya amince da nadin Lawal Maradun a matsayin sabon babban sakatarensa, PPS, inji rahoton kamfanin dillancin labaru.

Sakataren watsa labaru na gwamnan, Jamilu Iliyasu ne ya bayyana haka a ranar Juma’a a garin Gusau, inda yace gwamnan ya amince da nadin sabbin manyan sakatarori guda uku.

“Sabbin manyan sakatarorin sun hada da Alhaji Garba Ahmad, Alhaji Abubakar Jafar da kuma Alhaji Bala Umar.” Inji sanarwar.

Iliyasu ya kara da cewa Lawal Maradun ya kasance babban malamin a tsangayar ilimin jarida a kwalejin kimiyya da fasaha ta Abdu Gusa dake Talatan Mafara kafin wannan nadi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel