Zamfara: An zartar da hukuncin kisa a kan mutumin da ya kashe mahaifiyarsa da yan uwansa mata biyu

Zamfara: An zartar da hukuncin kisa a kan mutumin da ya kashe mahaifiyarsa da yan uwansa mata biyu

Wata babbar kotu a jihar Zamfara ta zartar da hukuncin kisa ta hanyar rataya a kan wani mutum da ya kashe mahaifiyarsa da yan uwansa mata biyu.

An gurfanar da Kamal Yusuf da wasu mutane biyu —Armayau Shehu da Caleb Humphrey a gaban kotu bisa zarginsu da aikata laifuka uku amma Humphrey ya mutu a gidan yari kafin a kammala sharia.

Laifukan da ake tuhumarsu da aikatawa sun hada da hadin baki, fashi da makami da kisa kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Da ya ke zartar da hukuncin, babban alkalin jihar, Mai sharia Kulu Aliyu ta yanke wa Kamal Yusuf hukuncin kisa ta hanyar rayata yayin da shi kuma mutum na biyu da ake tuhuma, Armayau Shehu an wanke shi an kuma sake shi.

DUBA WANNAN: Yadda wani mutum ya kashe dan uwansa saboda mangwaro (Hoto)

Wanda aka yanke wa hukuncin yana da ikon daukaka kara a cikin kwanaki 90.

Zamfara: An zartar da hukuncin kisa a kan mutumin da ya kashe mahaifiyarsa da yan uwansa mata biyu
Zamfara: An zartar da hukuncin kisa a kan mutumin da ya kashe mahaifiyarsa da yan uwansa mata biyu. Hoto daga Daily Trust
Asali: Twitter

A wani labarin, Rundunar Yan Sandan jihar Abia ta tabbatar da kama wani mutum mai matsakaicin shekaru, Chinedu Omeonu ya kashe dan uwansa, Solomon Monday Orji a garin Mgboko Umuoria a karamar hukumar Obingwa na jihar.

An gano cewa daya daga cikin yayan Orji ya shiga gidan kawunsa Chinedu Omeonu domin ya dauki wasu mangwarori da suka fado daga bishiya.

Omeonu sai ya kama dan Orji ya yi masa dukkan da har sai da ya sumar da shi. Sai Orji ya garzaya zuwa gidan dan uwansa domin ya ji dalilin da yasa ya zage dansa har sai da ya sumar da shi.

Wanda ake zargin ya fusata bayan Orji ya titsiye shi bisa dukan da ya yi wa dan sa, hakan yasa ya yi amfani da adda ya sare shi a lokacin da ya ke hanyarsa ta barin gidan.

Nan take Orji ya fadi ya mutu sakamakon raunin da dan uwansa ya masa da addar. Daga bisani matasa a garin sun yi wa Omeonu dukkan tsiya kafin suka mika shi hannun yan sanda.

Mai magana da yawun yan sandan jihar Abia, Geoffrey Ogbonna ya tabbatar da afkuwar lamarin kuma ya sanar da LIB cewa za a gurfanar da wanda ake zargin a kotu da zarar an kammala bincike.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel