Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga suna can sun kai hari a Katsina

Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga suna can sun kai hari a Katsina

A halin yanzu wasu yan bindiga suna can sun kai hari a garin Yankara da ke karamar hukumar Faskari na jihar Katsina.

Wani mazaunin garin da ya yi magana da SaharaReporters ya ce, "Suna can suna cin karensu ba babbaka a nan Yankara, suna kai wa mazauna kauyen hari, suna kone gidaje suna sace shanu."

Kimanin mutane 50 ne aka ruwaito cewa yan bindiga sun kashe a kananan hukumomin Kankara, Dutsinma, Musawa, Danmusa na jihar Katsina a cikin kwanaki 30 da suka shude.

Yanzu-yanzu: Yan bindiga suna can sun kai hari a Katsina
Yanzu-yanzu: Yan bindiga suna can sun kai hari a Katsina
Asali: Original

DUBA WANNAN: Yadda wani mutum ya kashe dan uwansa saboda mangwaro (Hoto)

A baya, mun kawo muku cewa a wani sautin murya da jaridar HumAngle ta samu, shugaban 'yan bindiga a Zamfara, Kachallah, ya ja kunnen mazauna Shinkafi da kada su kuskura su bar sojojin Najeriya a tsakaninsu.

Ya fitar da wannan sakon ne bayan tsanantar ayyukan dakarun sojin Najeriya a yankin don tarwatsa 'yan ta'addan.

Ya ja kunnen mutanen garin kamar haka, "Ta yaya sojoji za su dinga kashe min jama'a bayan tattaunawa muke. A kan mene za su fito neman 'yan bindiga?

"Na rantse da Ubangiji idan har suka kara kawo mana hari sai mun kashe 40 a nan, 50 a can, 30 a can kuma duk a rana daya. Na san za su so harar mu amma makoki ba zai bar su ba.

"Na rantse da Ubangiji, matukar kuka bar dakarun soji suka tsallako Shinkafi, ba za ku iya ciyar da 'yan gudun hijira ba,"

"Na basu kwana uku, idan basu daina ba, za mu zaba wasu yankuna. Sai mun kashe mutum 100 a Kurya. Za mu kori mutane daga yankuna masu tarin yawa.

"Abinda suke so shine mu ajiye makamai sannan mu tafi babu komai. Ai hakan ba za ta yiwu ba. Gara mu mutu kawai.

"Sun kwace mana sama da makamai 30, sun kwace mana babura sama da 60. Haka ake neman zaman lafiya?

"Muna jiran zuwan su. Ban je ko ina ba, ina jiran sojojin," in ji Kachallah.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164