Coronavirus: Garkuwar jikin marasa lafiya kawai muke bunkasa wa - Farfesa Alonge

Coronavirus: Garkuwar jikin marasa lafiya kawai muke bunkasa wa - Farfesa Alonge

Babban jagoran masu kula da cibiyoyin killace masu cutar korona a jihar Oyo, Farfesa Temitope Alonge, ya bayyana dabarar da su ke wajen warkar da masu cutar korona.

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, Farfesa Alonge ya yi karin haske dangane da yadda su ke kula da masu cutar korona har su samu waraka a cibiyoyin killace masu cutar da ke fadin jihar.

Farfesa Alonge, wanda shi ne tsohon shugaban Asibitin Koyarwa na Jami'ar Ibadan, ya ce hobbasan da ma'aikatan lafiya ke yi shi ne kawai neman bunkasa garkuwar jikin marasa lafiyan da aka kawo cibiyoyin killace masu cutar korona.

Ya ce akwai sanannun hanyoyi da tsare-tsaren inganta garkuwar jiki, sai dai a jihar Oyo sun riki tsari daya da ya ke taimaka musu wajen kara yawan mutanen da ke warkewa daga cutar korona a cibiyoyin da aka kula da su a fadin jihar.

Sai dai ya gargadi mutane da su sani cewa, duk da cutar korona tana cikin rukunin kwayoyin cututtuka masu yaduwa, sai dai ta banbanta ta kowace irin siga da sananniyar cutar nan mai karya garkuwar jiki wato cutar sida (HIV).

Coronavirus: Garkuwar jikin marasa lafiya kawai muke bunkasa wa - Farfesa Alonge

Coronavirus: Garkuwar jikin marasa lafiya kawai muke bunkasa wa - Farfesa Alonge
Source: Facebook

Wannan karin haske na Farfesa Olonge ya zo ne a ranar Juma'a, yayin sallamar wasu mutum 11 da suka warke daga cutar korona a cibiyar killacewa ta Olodo da ke birnin Ibadan.

Sanadiyar yadda kawo yanzu ba a samar da maganin cutar korona ba, a halin yanzu dai ingantacciyar garkuwar jiki ita kadai ce ke iya yakar cutar a jikin mutum kamar yadda mahukuntan lafiya suka bayyana.

KARANTA KUMA: Kyauta muka samu maganin cutar korona na kasar Madagascar - Boss Mustapha

A yayin da duniya ke ci gaba da fama da annobar korona, kwararren masanan kayan abinci da sha, sun ce akwai bukatar mutane su yi riko da kayan lambu da kuma 'ya'yan itatuwa domin inganta garkuwar jikinsu.

A halin yanzu dai bincike ya tabbatar da cewa, raunin garkuwa jiki yana da babbar alaka da tsufa yayin da a dukkanin kasashen da cutar korona ta bulla, ta fi kassara dattawa wadanda suka haura shekaru 60 a duniya.

Haka kuma bincike ya nuna cewa cutar korona ta fi kassara mutanen da suke fama da wasu cututtukan na daban kamar cutar daji, ciwon koda, ciwon suga hawan jini da sauransu.

'Ya'yan itatuwa da kayan lambu wadanda masu bincike suka tabbatar da ribar da suka kunsa ta bunkasa garkuwar jiki sun hadar da; ayaba, karas, mangwaro, tufa, tumatir, abarba, kashu, kankana, lemun zaki, gwanda, goba, da agwaluma.

Sun kuma ba da shawarar a yi riko da korayen ganyayyaki da suka kunshi sunadaran antioxidants kamar; vitamins A, vitamins C, vitamins E, beta carotene, da selenium.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel