Hotunan gidajen Diezani da aka mayar da su cibiyoyin killace masu COVID-19

Hotunan gidajen Diezani da aka mayar da su cibiyoyin killace masu COVID-19

Hukumar Yaki da Rashawa ta Najeriya, EFCC, ta mika gidajen da ta kwace daga hannun tsohuwar ministan man fetur, Diezani Alison-Madueke, don ayi amfani da su a matsayin cibiyoyin killace masu jinyar COVID-19.

Hukumar yaki da rashawar ta mika wa jamian gwamnatin jihar Legas wasu gidajen ne a ranar Juma'a kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Gidajen na Diezani sun hada da manyan gidaje wato flat masu dakunan kwana uku da kuma dakin samari da Diezani ta mika wa gwamnati sakamakon hukunci da babban kotun tarayya ta yanke a 2017.

Yanzu yanzu: EFCC ta bayar da gidajen Diezani a matsayin cibiyoyin killace masu korona

Yanzu yanzu: EFCC ta bayar da gidajen Diezani a matsayin cibiyoyin killace masu korona
Source: UGC

Yanzu yanzu: EFCC ta bayar da gidajen Diezani a matsayin cibiyoyin killace masu korona

Yanzu yanzu: EFCC ta bayar da gidajen Diezani a matsayin cibiyoyin killace masu korona
Source: UGC

Da ya ke magana a wurin bikin mika gidajen, Shugaban EFCC na Legas, Mohammed Rabo ya ce hukumar ta yi hakan ne a matsayin gudunmawa da za ta bawa mutane wurin yaki da annobar.

DUBA WANNAN: Yadda wani mutum ya kashe dan uwansa saboda mangwaro (Hoto)

Ya ce, "Baya ga aikin mu na yaki da rashawa, hukumar a shirye ta ke da taimaka da duk wani aiki da za ta iya yi domin yaki da annobar COVID-19.

"Saboda haka, kofar mu a bude ya ke a kowanne lokaci za mu amsa kira idan gwamnatin jihar Legas ta nemi mu taimaka da wani aikin da mutane ke bukata."

Sanarwar ta mai magana da yawun EFCC, Dele Oyewale ya fitar ya ce gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya mika godiyarsa ga hukumar ta yaki da rashawar.

Gwamnan ya ce yana maraba da wannan hadin gwiwar tsakanin gwamnatinsa da hukumar ta yaki da rashawar.

Bayan bayar da tabbacin cewa za ayi amfani da gidajen ta hanyoyin da suka dace, gwamnan ya mika godiyarsa ga hukumar saboda mayar da hankali kan yunkurin da jihar ke yi na dakile cutar.

Ya kara da cewa rashin isasun cibiyoyin killace masu jinya na daya daga cikin kallubalen da jihar ke fuskanta wurin yaki da annobar ta korona.

Legas, wacce ke cikin jihohin da suke kan gaba wurin yawan mutanen da suka kamu da COVID-19 tana fama da karancin gadon asibiti don ba wa masu jinyar ta korona.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel