'Yan Najeriya za su fara karbar hayar mazubin gas din girki – FG

'Yan Najeriya za su fara karbar hayar mazubin gas din girki – FG

Gwamnatin Tarayya a ranar Alhamis ta sanar da cewa za ta samar da wasu cibiyoyin da masu amfani da iskar gas wurin girki za su rika sayan gas din tare da kabar hayar mazubin gas din wato cylinder.

Ta kuma ce Hukumar Man Fetur ta Najeriya, NNPC, da sauran dillalan man fetur za su fara sayar da saka famfon iskar gas na girki a gidajen mai domin jan hankulan yan Najeriya su dena amfani da fetur a ababen hawa su koma gas.

Karamin ministan man fetur na Najeriya, Timipre Sylva ne ya sanar da hakan a Abuja, ya kuma kara da cewa gwamnati ta cire hannun ta cikin harkokin tace man fetur da sayar da shi.

Shugaban hukumar NNPC, Myele Kyari ya kuma sanar da annobar COVID-19 ya janyo jinkiri wurin aikin gyaran matatan man fetur na Fatakwal.

'Yan Najeriya za su fara karbar hayar mazubin gas din girki – FG
'Yan Najeriya za su fara karbar hayar mazubin gas din girki – FG. Hoto daga The Cable
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Yadda wani mutum ya kashe dan uwansa saboda mangwaro (Hoto)

Sylva ya ce gwamnati na kokarin ganin yan Najeriya sun dena amfani da kalanzir wurin girki sun koma gas shiyasa ta bullo da wannan shirin.

Ya ce, "Dalilin da yasa mutane ba su cika amfani da gas sosai ba saboda tsadar sayan mazubin ne da ke yi wa talaka wahala.

"Abinda mu ke son yi shine mu ga yadda za muyi mutane su samu mazubin gas din cikin sauki ba tare da sun kashe kudi mai yawa ba a lokaci guda."

Ya cigaba da cewa, "Idan mun samar da wannan muna fatan ganin gasa tsakanin iskar gas da sauran makamashin girki dama abinda yasa kalanzir ke da sauki shine mutum ko bashi da kudi yana iya sayan kwalba daya ya yi amfani da shi."

"Amma idan mun samar da wannan tsarin, gas zai yi araha sosai kuma muna fatan mutane da yawa za su fara amfani da shi."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel