Yanzu amfani da takunkumin rufe fuska ya zama tilas - Gwamnatin Tarayya

Yanzu amfani da takunkumin rufe fuska ya zama tilas - Gwamnatin Tarayya

A ranar Alhamis, 15 ga watan Mayu, gwamnatin tarayya ta ce a yanzu sanya takunkumin rufe fuska ya zama tilas ga dukkanin al'umma a fadin kasar nan.

Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, shi ne ya sanar da hakan a ranar da ta gabata cikin babban birnin kasar na tarayya.

Mista Mustapha shi ne shugaban kwamitin da fadar shugaban kasa ta kafa domin lura da annobar korona a Najeriya.

Sanarwarsa ta zo a yayin zaman karin haske kashi na 31 kan halin da ake ciki dangane da cutar korona a kasar.

Ya ce a yanzu amfani da takunkumin rufe fuska ba ra'ayi bane sai dai ya zama tilas gami da samun madogara ta shari'a.

Sakataren Gwamnatin Tarayya; Boss Mustapha
Sakataren Gwamnatin Tarayya; Boss Mustapha
Asali: UGC

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, sakataren gwamnatin ya kirayi hukumomin tsaro da su tabbatar da al'ummar Najeriya sun kiyaye wannan doka.

Sakataren gwamnatin yana mai cewa, a halin yanzu yin amfani da takunkumin rufe fuska ya kasance daya daga cikin hanyoyin dakile yaduwar cutar korona wadda tuni shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya sanya ta a cikin dokokin kasar.

KARANTA KUMA: Falalar kwanaki goman karshe na watan Ramadan

Ya nemi gwamnonin jihohi 36 na tarayyar Najeriya da su tabbatar da al'ummominsu sun kiyaye wannan doka da za ta taka rawar gani wajen 'mu gudu tare kuma tsira tare'.

Babu shakka mahukuntan lafiya sun tabbatar da cewa, tukunkumin rufe fuska wani shinge ne da ake amfani da shi wajen hana kamuwa da cututtuka masu yaduwa ta hanyar tari, atishawa ko kuma yawun baki.

Yayin da gwamnatin Najeriya ta fara shirye-shiryen rage tsaurin dokar hana zirga-zirga, ta shimfida matakan dakile yaduwar cutar korona da suka hadar da sanya takunkumin rufe fuska da kuma ba da tazara yayin shiga cikin jama'a.

Alkaluman da Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka a Najeriya NCDC ta fitar a ranar Alhamis sun nuna cewa, ya zuwa yanzu cutar korona ta harbi mutum 5,162 a duk fadin kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel