Covid-19: Tsohuwa mai shekaru 108 ta warke daga korona a Amurka

Covid-19: Tsohuwa mai shekaru 108 ta warke daga korona a Amurka

Wata tsohuwa mai shekaru 108 a kasar Amurka, Sylvia Goldsholl da ta yi rayuwa zamanin da aka yi annobar murar 1918 ta warke daga coronavirus kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Phil Murphy, gwamnan New Jersey ne ya bayyana labarin a ranar Alhamis inda ya ce Goldsholl ta warke sarai bayan kamuwa da cutar a watan Afrilu.

Gwamnan ya ce, "Shekarun Sylvia Goldsholl 108, ta kamu da Covid-19 kuma ta warke."

Gwamna Murphy ya aike mata da sakon taya murna da fatan alheri bisa warkewar da ta yi.

Goldsholl wacce ke zaune a gidan kulawa da tsofaffi a Allendale, New Jersey ita ce mutum mafi tsufa da ta warke daga cutar a jihar ta.

Covid-19: Tsohuwa mai shekaru 108 ta warke daga korona

Covid-19: Tsohuwa mai shekaru 108 ta warke daga korona. Hoto daga The Cable
Source: UGC

DUBA WANNAN: Yadda wani mutum ya kashe dan uwansa saboda mangwaro (Hoto)

"Na warke ne saboda ban taba cire tsammani ba," in ji ba amurkiyar da aka ce shekarun ta bakwai lokacin da annobar murar 1918 yadu a kasashen duniya kamar yadda News 12 ta ruwaito.

Warkewarta ya zama abin misali a duniya duba da cewa masana sun bayyana cewa cutar ta fi kashe mutane masu yawan shekaru.

Maria Branyas, mai shekaru 113 yar kasar Spain ita ce wadda ake ganin babu wanda ya dara ta a shekaru cikin wadanda suka warke daga cutar.

A wani labarin daban, kun ji cewa Kwamishinan Muhalli da Albarkatun kasa na jihar Oyo, Mr Kehinde Ayoola ya rasu.

Ya rasu yana da shekaru 55 a duniya. Ayoola, tsohon kakakin majalisar jihar ta Oyo, ya yi fama da rashin lafiya na kimanin sati biyu.

Ya rasu ne a wani asibiti mai zaman kansa a Iyaganku a garin Ibadan inda ake masa magani. Dan siyasan haifafar garin Oyo ya wakilci mazabar Oyo ta Gabas daga shekarar 1999 and 2003.

An haifi Ayoola ne a ranar 14 ga watan Janairu a garin Oyo na jihar Oyo. Ya yi karatun digir a Jamiar Obafemi Awolowo da ke Ile Ife.

Ya yi karatun nazarin kimiyyar dabobi da kula da muhalli. Ya auri Olukemi, mataimakiyar Farfesa a tsangayar nazarin aikin noma. Kuma suna da yara biyu.

Taiwo Adisa, mai magana da yawun gwamnan jihar Oyo Rotimi Makinde shima ya tabbatar da rasuwar kwamishinan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel