Innalillahi wa inna ilaihi raji’un: Allah Ya yi ma Tafidan Ilori rasuwa

Innalillahi wa inna ilaihi raji’un: Allah Ya yi ma Tafidan Ilori rasuwa

Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, Allah Ya yi ma Tafidan Ilorin, Dakta Amuda Aluko rasuwa, kamar yadda jaridar Sahara Reporters.

Rahotanni sun bayyana Aluko dan shekara 85 ya rasu ne da sanyin safiyar Juma’a, 15 ga watan Mayu bayan fama da yayi da rashin lafiya.

KU KARANTA: Minista Sadiya Umar Farouk ta bayyana tsarin da suke bi wajen ciyar da dalibai a gida

An haifi Aluko a watan Oktoban shekarar 1935 a gidan Apabiekun dake karamar hukumar Ilori ta yamma, kuma babban likita wanda ya kafa asibitinsa mai suna Geri Alimi Hospital Ilorin.

Cikin wani hira da ya yi da jaridar Daily Trust a shekarar 2019, Amuda ya bayyana cewa bai san takamaimen shekarunsa ba, amma dai an fada masa a shekarar 1935 aka haife shi.

Innalillahi wa inna ilaihi raji’un: Allah Ya yi ma Tafidan Ilori rasuwa
Amuda Hoto: Dailt Trust
Asali: UGC

“Na yi makarantu dayawa, tun daga makarantar Middle ta Ilorin a shekarar 1949, daga nan na zarce kwalejin Barewa ta Zaria, daga Zaria na koma kwalejin tsaftar muhalli ta Kano inda na yi shekaru biyu.

“A lokacin da gwamnatin lardin Arewa ke bukatar kafa kwalejin likitanci, ina daya daga cikin daliban da aka fara dauka, muna da yawa wadanda muka fara, amma mu hudu kawai muka gama.

“Daga nan aka aika ni zuwa birnin Landan don karin karatu, a shekarar 1968 na tafi kwalejin tsaftar muhalli da kiwon lafiya dake Landan. Daga nan hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO ta dauke ni zuwa kasar Masar, ina dawowa aka kai ni Okene don yin aiki.” Inji shi.

A wani labari kuma, Gwamnatin jahar Kwara ta sallami babban sakataren ma’aikatar kiwon lafiya na jahar, Dakta Ayinla Abubakar biyo bayan sakaci da yayi wajen gudanar da aikinsa.

Mataimakin gwamnan jahar, kuma shugaban kwamitin yaki da cutar COVID19 a jahar, Kayode Alabi ne ya bayyana haka a ranar Alhamis.

Alabi yace Abubakar ya bada umarnin daukan wani mutumi mai kama da mahaukaci ne a cikin motar da ake daukan masu cutar COVID19 ba tare da cika ka’idojin da aka gindaya ba.

Alabi ya bayyana sakacin da Ayinla ya nuna a matsayin abin kunya, musamman duba da cewa shi ne babban sakataren ma’aikatar kiwon lafiya, kuma memba a kwamitin yaki da cutar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: