Buhari ya jinjina ma ma’aikatan kiwon lafiya da suka kula da Sarkin Daura

Buhari ya jinjina ma ma’aikatan kiwon lafiya da suka kula da Sarkin Daura

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana farin cikinsa da samun labarin lafiyar da mai martaba Sarkin Daura, Alhaji Farouk Umar Farouk yake samu.

Gidan talabijin na Channels ta ruwaito baya ga farin cikin da Buhari ya nuna game da lafiyar Sarki, shugaban ya jinjina ma ma’aikatan kiwon lafiyan da suka kula da Sarkin.

KU KARANTA: Minista Sadiya Umar Farouk ta bayyana tsarin da suke bi wajen ciyar da dalibai a gida

“Na ji dadin samun labarin nasarar da aka samu wajen kulawa da kai, tare da sallamarka da aka yi daga asibiti bayan kwanaki 10 kana jinya. Duba da lokacin da muke ciki, mun shiga damuwa kwarai game da kai. Don haka na yi farin ciki sosai da ka fito da koshin lafiyarka.” Inji shi.

Buhari ya jinjina ma ma’aikatan kiwon lafiya da suka kula da Sarkin Daura
Buhari da Sarkin Daura Hoto: PremiumTimes
Asali: UGC

Haka zalika shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yaba da kokarin da jami’an kiwon lafiya suka yi wajen kulawa da Sarkin a cibiyar kiwon lafiya ta gwamanatin tarayya dake Katsina.

Bugu da kari shugaba Buhari ya jinjina ma sauran jami’an kiwon lafiya dake kula da sauran marasa lafiya dake dukkanin asibitocin dake fadin Najeriya.

“Najeriya ta yi sa’an samun jajirtattun ma’aikatan kiwon lafiya. Za mu cigaba da daukan duk matakan da suka kamata don kara musu karfin gwiwa.” Inji shugaba Buhari.

A wani labari kuma, Wata karamar yarinya yar shekara 6 ta rabu da cutar Coronavirus mai toshe numfashi a jahar Jigawa.

Yarinyar, yar asalin garin Kazaure an sallameta daga cibiyar killace masu cutar Coronavirus dake garin Dutse ne tare da mahaifinta, wanda daga wajensa ta samu cutar.

Rahoton gidan talabijin na Channels ta bayyana cewa mahaifin yarinyar ya yi tafiya zuwa jahar Enugu ne, inda dawowarsa gida Kazaure aka gane yana dauke da cutar.

Kuma wannan mutumi shi ne na farko da ya fara kamuwa da cutar a garin Kazaure gaba daya, kamar yadda kwamishinan jahar kiwon lafiya na jahar, Abba Zakari ya bayyana.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng