Yadda wani mutum ya kashe dan uwansa saboda mangwaro (Hoto)

Yadda wani mutum ya kashe dan uwansa saboda mangwaro (Hoto)

Rundunar Yan Sandan jihar Abia ta tabbatar da kama wani mutum mai matsakaicin shekaru, Chinedu Omeonu ya kashe dan uwansa, Solomon Monday Orji a garin Mgboko Umuoria a karamar hukumar Obingwa na jihar.

An gano cewa daya daga cikin yayan Orji ya shiga gidan kawunsa Chinedu Omeonu domin ya dauki wasu mangwarori da suka fado daga bishiya.

Omeonu sai ya kama dan Orji ya yi masa dukkan da har sai da ya sumar da shi.

Sai Orji ya garzaya zuwa gidan dan uwansa domin ya ji dalilin da yasa ya zage dansa har sai da ya sumar da shi.

Yadda wani mutum ya kashe dan uwansa saboda mangwaro

Yadda wani mutum ya kashe dan uwansa saboda mangwaro
Source: UGC

DUBA WANNAN: JAMB: Jihohi 5 da ke kan gaba wajen magudin jarabawar 2020

Wanda ake zargin ya fusata bayan Orji ya titsiye shi bisa dukan da ya yi wa dan sa, hakan yasa ya yi amfani da adda ya sare shi a lokacin da ya ke hanyarsa ta barin gidan.

Nan take Orji ya fadi ya mutu sakamakon raunin da dan uwansa ya masa da addar.

Daga bisani matasa a garin sun yi wa Omeonu dukkan tsiya kafin suka mika shi hannun yan sanda.

Mai magana da yawun yan sandan jihar Abia, Geoffrey Ogbonna ya tabbatar da afkuwar lamarin kuma ya sanar da LIB cewa za a gurfanar da wanda ake zargin a kotu da zarar an kammala bincike.

A wani labarin, mun kawo muku cewa Rundunar Yan sanda ta jihar Sokoto ta kama mutum 155 daga karfe 8 na daren ranar Laraba zuwa karfe 6 na ranar Alhamis da suka saba dokar kulle da aka saka a jihar don dakile yaduwa annobar COVID-19.

Wannan na cikin wata sanarwa ce ta mai magana da yawun rundunar, Muhammad Sadiq, mai mukamin mataimakin superintendent na yan sanda ya fitar a ranar Alhamis a Sokoto kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Mr Sadiq ya ce twagar hadin gwiwa ta jamian tsaro karkashin jagorancin kwamishinan Yan sandan jihar, Ibrahim Kaoje, daga ranar 5 ga watan Mayu zuwa 14 ga watan Mayu ta kama motoci da babura a kalla 63.

Ya bayyana cewa rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wurin kama duk wani mutum ko kungiya ta aka samu da saba dokar ta hana fita.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel