Almajirai ne dandalin cutar korona - Ganduje

Almajirai ne dandalin cutar korona - Ganduje

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya kwatanta Almajirai da dandalin cutar coronavirus saboda rashin tsafta, wurin zama da kuma rashin kula da kai.

Saboda suna zama wurin cunkoso, basu da takamaiman wurin bacci, ba su samun abincin da ya dace kuma babu tsafta, shiyasa suka fi kamuwa, gwamnan yace kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

A saboda haka, Ganduje ya yanke hukuncin mayar da hankali wajen kafa kungiyar taimakon gaggawa don dubawa tare da bada kariya garesu saboda annobar nan.

Kamar yadda gwamnan ya bayyana, wadanda aka samu basu dauke da cutar, za a mika su ga iyayensu yayin da za a tsare wadanda ke da ita har sai sun warke. Bayan samun warakar, za a mayar da su jihohinsu tare da shaidar NCDC.

Ya ce, "mun yanke shawarar gwada dukkan almajiran jihar Kano. Niyyar mu shine basu kariya. Duk wadanda basu dauke da cutar za mu mayar da su jihohinsu yayin da masu dauke da cutar za a basu magani tare da shaidar NCDC ta warakar su.

Almajirai ne dandalin cutar korona - Ganduje

Almajirai ne dandalin cutar korona - Ganduje. Hoto daga The Cable
Source: Twitter

KU KARANTA: Turmi da tabarya: Matar aure ta mutu yayin da Fasto ke lalata da ita a gidansa

"Ga almajiran da ke Kano kuwa, mun shirya ilimantar da su. Ga wadanda basu da wurin zuwa, mune iyayensu kuma za mu kula da su.

"Niyyar mu ita ce tabbatar da an hade karatun Almajiri da na Boko. Yaranmu na da hakkin samun ilimi, hakazalika almajirai."

A wani labari na daban, Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya sanar da isowar wata kungiyar 'yan ta'adda mai suna Darus Salam jiharsa, wacce ya kwatanta da kungiya mai tarin hadari.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa jihar Nasarawa na cikin matsanancin halin matsalar tsaro a cikin kwanakin nan.

Sabuwar kungiyar ta kware a garkuwa da manyan mutane na jihar kamar su mai bada shawara na musamman ga gwamnan jihar, sarakuna, sakatarorin gwamnati da sauransu.

A yayin zantawa da manema labarai jim kadan bayan tattaunawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari, gwamnan ya danganta garkuwa da mutane da kuma kashe-kashen da ake da kungiyar.

Kamar yadda yace, da farko kungiyar ta bar jihar amma da ta tashi dawowa sai ta iso da sabon karfinta inda ta sauka a wasu kananan hukumomi na jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel