Ta fallasu: Kun san jikakkiyar da ke tsakanin Ganduje da El-Rufai?

Ta fallasu: Kun san jikakkiyar da ke tsakanin Ganduje da El-Rufai?

Boyayyar da ke tsakanin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano da Malam Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ta bayyana a makonni biyu da suka gabata.

Gwamnan Kano din ya mayar wa takwaransa na jihar Kaduna zazzafan martani a kan maganar korona da almajirai ke kaiwa jihar Kaduna.

Malam Nasir El-Rufai ya maimaita cewa mafi yawan masu korona a jiharsa almajirai ne daga jihar Kano wadanda Ganduje ya dawo mishi da su.

Wannan maganar ta matukar fusata Ganduje inda ya mayar da martani yana cewa, "Yadda muke mayar da almajirai jihohinsu, haka ake dawo mana da almajirai 'yan asalin jihar Kano gida.

"Rashin surutu da muke yi a akan hakan ba yana nufin dukkansu lafiyarsu kalau ake dawo mana da su ba ko suna dauke da cutar."

Ta fallasu: Kun san jikakkiyar da ke tsakanin Ganduje da El-Rufai?
Ta fallasu: Kun san jikakkiyar da ke tsakanin Ganduje da El-Rufai? Hoto daga BBC Hausa
Asali: Twitter

KU KARANTA: Darus Salam: Sabuwar kungiyar ta'addanci da ta sauka a Arewa

Amma abun tambayar shine, yaushe Malam suka raba hanya da Ganduje?

Malam Kabiru Sufi masanin kimiyyar siyasa ne a garin Kano. Ya shaida wa BBC cewa alakar da ke tsakanin gwamnonin biyu ta jike ne bayan Gwamna Ganduje ya yi kunnen uwar shegu da alfarmar da El-Ruafi ya nema.

Malam ya roki takwaran sa da kada ya tube wa amininsa rawani, lamarin da ya yi kamar ba da shi ake ba.

An gano cewa manyan jam'iyyar APC sun dage wajen kokarin sulhu tsakanin Gwamna Ganduje da Sarki Sanusi amma hakan bai yuwu ba.

Sufi ya ce, "Ina kyautata zaton wannan abu bai yi wa El-Rufai dadi ba, kuma daga nan ne alakar ta jike.

"Kafin wannan lamarin ya faru, sanannen abu ne idan aka ce Bola Tinubu da Malam Nasir sun taka rawar gani wajen tabbatar da zarcewar Ganduje."

Babu dadewa da tube rawanin Sanusi, Malam Nasir ya ba shi mataimakin KADIPA. Washegari kuwa ya nada shi uban jami'ar jihar Kaduna.

Bayan kimanin mako daya, Malam Nasir ya kai wa amininsa ziyara garin Awe da ke jihar Nasarawa. Ya raka shi har garin Abuja inda ya hau jirgi ya nufi jihar Legas inda iyalansa suke.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel