Almajirai 28 sun kamu da korona a Jigawa

Almajirai 28 sun kamu da korona a Jigawa

Gwamnatin Jihar Jigawa ta ce Almajirai guda 28 sun kamu da kwayar cutar COVID-19 da aka fi sani da coronavirus a jihar kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Hakan ya kawo adadin almajiran da suka kamu da kwayar cutar ta COVID-19 zuwa 31 a Jigawa cikin kwanaki biyu da suka gabata.

A ranar 13 ga watan Mayun 2020, Hukumar Kiyaye Cututtuka Masu Yaduwa, NCDC ta tabbatar da mutum 141 da suka kamu da cutar a jihar.

Almajirai 28 sun kamu da korona a Jigawa
Almajirai 28 sun kamu da korona a Jigawa. Hoto daga The Cable
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Zamfara: Shugaban 'yan bindiga ya fitar da sautin murya, ya ja kunnen jama'a da kakkausar murya

Abba Zakari, Kwamishinan Lafiya na jihar wanda shine kuma shugaban kwamitin kar ta kwana na yaki da annobar korona ta jihar Jigawa ya tabbatar da sabbin wadanda suka kamu da cutar a ranar Alhamis a Dutse.

A cewarsa, hakan ya kawo jimillar wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar a jihar yanzu 169, cikin su uku sun mutu.

"A ranar Laraba, NCDC ta fitar da alkaluman sabbin wadanda suka kamu da cutar kuma ka san muna aiki ne da dakin gwaji a Kaduna don yi wa almajiran da aka dawo mana da su Jigawa gwaji," a cewar Kwamishinan.

"Baya ga sabbin mutum 23 da suka kamu, mun kuma samu wasu karin almajirai 28 da suka kamu da cutar.

"A cikin 23 da NCDC ta sanar, uku daga cikinsu almajirai ne, hakan ya kawo jimillar 51. Kuma cikin 51, 31 daga ciki almajirai ne."

Ya kara da cewa nan da kwanaki kadan, gwamnatin jihar za ta kafa sabuwar dakin gwaji a babban asibitin Dutse da ke babban birnin jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel