Annobar Coronavirus: Gwamnan Kwara ya kori babban jami’in gwamnati saboda sakaci da aiki

Annobar Coronavirus: Gwamnan Kwara ya kori babban jami’in gwamnati saboda sakaci da aiki

Gwamnatin jahar Kwara ta sallami babban sakataren ma’aikatar kiwon lafiya na jahar, Dakta Ayinla Abubakar biyo bayan sakaci da yayi wajen gudanar da aikinsa.

Jaridar Punch ta ruwaito mataimakin gwamnan jahar, kuma shugaban kwamitin yaki da cutar COVID19 a jahar, Kayode Alabi ne ya bayyana haka a ranar Alhamis.

KU KARANTA: Aiki tukuru: Buhari ya zayyana wasu manyan ayyuka da zai gudanar bayan an shawo kan Coronavirus

Alabi yace Abubakar ya bada umarnin daukan wani mutumi mai kama da mahaukaci ne a cikin motar da ake daukan masu cutar COVID19 ba tare da cika ka’idojin da aka gindaya ba.

Alabi ya bayyana sakacin da Ayinla ya nuna a matsayin abin kunya, musamman duba da cewa shi ne babban sakataren ma’aikatar kiwon lafiya, kuma memba a kwamitin yaki da cutar.

Annobar Coronavirus: Gwamnan Kwara ya kori babban jami’in gwamnati saboda sakaci da aiki

Gwamnan Kwara Hoto:Punch
Source: UGC

“Kwamitinmu ta ji kunyar abin da ya faru, mun dakatar da direban daya tuka motar daga duk wasu ayyukan da muke gudanarwa na yaki da COVID19, shi kuwa babban sakataren daya bashi umarnin daukan mutumin ba tare da jiran yan kwana kwanan mu ba, mun dakatar da shi daga aiki

“Bamu gamsu da bayanan da ya bamu dangane da lamarin ba, don haka mun umarce shi ya mika ragamar iko ga jami’i mafi girma a kwamitin, wannan yasa dole ne mu sake horas da direbobin dake aiki da kwamitin don kada a sake samun irin haka.” Inji shi.

A wani labarin kuma, Duk da hauhawar adadin mutanen da Coronavirus ta ke kamawa a Najeriya, an samu wasu jahohin Arewa biyar da suka bude Masallatai don a cigaba da Sallah.

Wannan mataki baya rasa nasaba da kiraye kiraye da jama’a suka dinga yi ga gwamnatocin jahohi, musamman a yankin Arewacin Najeriya na cewa a bude Masallatai don a roki Allah.

Wasu kuma na ganin ina amfanin an bude kasuwanni, inda dubun dubatan mutane ke taruwa, amma kuma a kasa bude wuraren bauta wanda basu tara jama’an da kasuwanni ke tarawa?

Jahohin sun hada da Kogi, Zamfara, Gombe, Borno da kuma jahar Adamawa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel