Dubi wasu jahohin Arewacin Najeriya 5 da suka bude Masallatai don a cigaba da Sallah

Dubi wasu jahohin Arewacin Najeriya 5 da suka bude Masallatai don a cigaba da Sallah

Duk da hauhawar adadin mutanen da Coronavirus ta ke kamawa a kullum a Najeriya, an samu wasu jahohin Arewacin Najeriya guda biyar da suka bude Masallatai don a cigaba da Sallah.

Wannan mataki baya rasa nasaba da kiraye kiraye da jama’a suka dinga yi ga gwamnatocin jahohi, musamman a yankin Arewacin Najeriya na cewa a bude Masallatai don a roki Allah.

KU KARANTA: Aiki tukuru: Buhari ya zayyana wasu manyan ayyuka da zai gudanar bayan an shawo kan Coronavirus

Wasu kuma na ganin ina amfanin an bude kasuwanni, inda dubun dubatan mutane ke taruwa, amma kuma a kasa bude wuraren bauta wanda basu tara jama’an da kasuwanni ke tarawa?

Dubi wasu jahohin Arewacin Najeriya 5 da suka bude Masallatai don a cigaba da Sallah

Masallaci Hoto: ChannelsTV
Source: Twitter

Legit.ng ta tattaro muku wadannan jahohin Arewacin Najeriya biyar da suka baiwa jama’an daman cigaba da gudanar da sallolinsu duk da matsalar Corona da ake fama da ita.

Kogi: Gwamnan jahar Kogi Yahaya Bello ne ya fara umartar a bude Masallatai a jahar, bayan an garkame su saboda tsoron yaduwar cutar Coronavirus.

Gwamnan ta bakin kwamishinan watsa labaru Kingsley Fanwo ya yi kira ga shuwagabannin addinai su sanya tsare tsaren kariya tare da kiyaye yaduwar cutar a wuraren ibada.

Sa’annan ya yi kira ga shuwagabannin addinai su cigaba da yin addu’o’i don ganin an shawo kan cutar a duniya gaba daya.

Borno: Gwamnan jahar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya sanar da janye dokar hana zirga zirga a jahar bayan kwashe makonni uku a cikinta.

Mataimakin gwamnan jahar, kuma shugaban kwamitin yaki da COVID-19 a jahar, Usman Kadafur ne sanar da janye dokar, inda yace sun cimma manufarsu ta sanya dokar tun a farko.

“An janye dokar, amma idan aka sake samun matsalar yaduwar cutar, zamu koma gidan jiya, dole ne a sanya takunkumin kariya, za’a cigaba da gudanar da sallar Juma’a da sauran salloli kamar yadda aka saba a Masallatai tare da dabbaka ka’idar tsayawa nesa nesa.” Inji shi.

Gombe: Gwamna Inuwa Yahaya na jahar Gombe ya sanar da janye dokar kulle Masallatai don yaki da yaduwar cutar COVID-19 bayan wata ganawa da yayi da shuwagabannin addinai.

Gwamnan yace Malamai sun tabbatar masa da aniyarsu ta tabbatar da mabiyansu sun bi dokokin da gwamnati ta gindaya na kariya daga cutar tare da kare yaduwarta.

Amma ya gargadesu idan suka yi sakaci da bin dokokin da aka shimfida na sanya takunkumi da tsayawa nesa nesa, zai mayar da dokar.

Adamawa: Gwamna Umar Fintiri na jahar Adamawa ya baiwa Musulmai daman su cigaba da gudanar ibadunsu a Masallatai kamar yadda aka saba.

Kakaakin gwamnan, Humwashi Wonosikou ne ya bayyana haka a ranar Alhamis, inda yace gwamnan ya nemi Malamai su tabbatar da tsarin kare yaduwar cutar a wuraren bauta.

“Za’a iya bude Masallatai, Coci Coci da kasuwannin dabbobi.” Inji shi.

Zamfara: Gwamna Bello Matawalle ya bada umarnin a cigaba da gudanar Salloli a Masallatai a duk fadin jahar bayan janye dokar hana hakan da yayi saboda tsoron yaduwar COVID-19.

Matawalle ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa daya fitar da kansa a gidan rediyon jahar a ranar Alhamis inda ya gode ma jama’a bisa yin biyayya ga dokokin da aka sanya da suka yi.

“Saboda haka mun janye dokar hana bude Masallatai da Coci, amma muna kira ga al’umma kada a dinga taruwa dayawa a lokaci daya a wuraren ibada. Sa’annan a dinga sanya takunkumi.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel