Gwamnati ta gano biliyan N4.3 da aka boye tsawon shekaru 10 a wani asusun sirri

Gwamnati ta gano biliyan N4.3 da aka boye tsawon shekaru 10 a wani asusun sirri

Gwamnatin jihar Ondo ta bayyana yadda ta gano wasu makudan kudi har biliyan N4.3 da aka boye tsawon shekara 10 a wani asusu na sirri a banki.

A cewar gwamnatin jihar, an boye kudin ne a daya daga cikin bankunan zamani da ke kasar nan ba tare da bin ka'ida ba, sai yanzu aka dauko hayar wasu kwararru domin fitar da kudin daga asusun.

A cikin jawabin da ya fitar, kwamishinan yada labarai na jihar Ondo, Donald Ojogo, ya ce ''iya bin kwakwafi da sanin aiki na kwamishinan kudi, Wake Akinterinwa, ne ya kai ga gano makudan kudaden."

Ojogo ya ce kwamishinan kudin ya hanzarta sanar da gwamnatin jihar Ondo bayan ya gano boyayyun kudaden.

Ya ce yanzu haka an mayar da kudaden zuwa asusun gwamnatin jihar, inda za a yi amfani da su bisa tsarin gaskiya.

A cewarsa, "tun bayan shigowar wannan gwamnati mu ke kokari wajen warware dumbin matsalolin da muka gada, wanda suka hada da batun gano kadarori da dukiyoyin gwamnati.

Gwamnati ta gano biliyan N4.3 daka boye tsawon shekaru 10 a wani asusun sirri
Gwamnan jihar Ondo; Rotimi Akeredolu
Asali: UGC

"Mu na yin aiyukanmu ne ba tare da yawan kwarmato ko surutu ba, saboda ba ma son rudani da tayar da kura.

"Bankuna da sauran masu hulda da gwamnati a bangarori daban - daban sun bamu hadun kai, mu na godiya garesu.

DUBA WANNAN: Katsinawa sun kwaikwayi NCDC, sun fara fitar da alkaluman ta'adin 'yan bindiga a kullum

"Kwamishinan kudi da babban akanta na jiha ba sa kan mukamansu lokacin da aka boye wadannan kudade shekaru goma da suka gabata.

"Majalisar dokokin jiha ta gayyaci kwamishinan kudi, babban akanta da odita na jiha, ba don komai ba, sai don jin yadda aka gano makudan kudaden, wanda hakan ya yi daidai da tsarin gwamnatin jihar Ondo na gudanar da aiki ba tare da boye komai ba.

"Kwamishinan kudi ya sanar da majalisar cewa shine silar gano kudaden da aka boye a banki."

Ya kara da cewa kwamishinan ya shaidawa majalisar cewa an boye kudaden ne a wani asusun kudin shiga na gwamnatin jihar tare da musanta jita - jitar cewa wasu ma su bincike da aka dauko haya ne suka gano kudaden.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel