Yadda masu garkuwa da mutane suka tsere suka bar wadanda suka sace a daji
Masu garkuwa da mutane da suka kama wani soja mai mukamim Kyaftin mai suna Gana sun yi watsi da mutanen da suke garkuwa da su a cikin daji sun tsere.
Rahoto ya bayyana cewa masu garkuwa da mutanen sun tsere ne yayin da jamian tsaro suke daf da isowa mabuyarsu a cikin daji kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Yan bindigan sun sace Gana da wasu mutanen ne a ranar Talata a kusa da garuruwan Auga-Akoko-Ibilo da ke kan iyakan jihohin Ondo da Edo.

Asali: Twitter
An gano su ne a wani daji da ke Ibilo a jihar Edo.
DUBA WANNAN: JAMB: Jihohi 5 da ke kan gaba wajen magudin jarabawar 2020
Mai magana da yawun rundunar sojoji ta 32 Artillery Brigade a Akure, Kyaftin Ayorinde ya ce tawagar sojoji da wasu jamian tsaro ne suka ceto sojan ba tare da an biya kudin fansa.
A wani rahoton, mun kawo muku cewa Rundunar Yan sanda ta jihar Sokoto ta kama mutum 155 daga karfe 8 na daren ranar Laraba zuwa karfe 6 na ranar Alhamis da suka saba dokar kulle da aka saka a jihar don dakile yaduwar annobar COVID-19.
Wannan na cikin wata sanarwa ce ta mai magana da yawun rundunar, Muhammad Sadiq, mai mukamin mataimakin superintendent na yan sanda ya fitar a ranar Alhamis a Sokoto kamar yadda Premium Times ta ruwaito.
Mr Sadiq ya ce twagar hadin gwiwa ta jamian tsaro karkashin jagorancin kwamishinan Yan sandan jihar, Ibrahim Kaoje, daga ranar 5 ga watan Mayu zuwa 14 ga watan Mayu ta kama motoci da babura a kalla 63.
Ya ce, "An gudanar da ingattacen binciken a kan kamen da aka yi kamar yadda kwamishinan yan sanda ya bayar da umurni kafin a kai su kotu."
Ya bayyana cewa rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wurin kama duk wani mutum ko kungiya ta aka samu da saba dokar ta hana fita.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng