Mutane 'yan shekaru 31 zuwa 40 sun fi saurin kamuwa da cutar korona - NCDC

Mutane 'yan shekaru 31 zuwa 40 sun fi saurin kamuwa da cutar korona - NCDC

Hukumar Kula da Yaduwar Cututtuka ta Najeriya NCDC, ta ce mutanen da ke tsakanin shekaru 31 zuwa 40 musamman maza sun fi saurin kamuwa da cutar korona a kasar.

Koda yake a cewar NCDC, an fi samun mace-macen dattawan mutane wadanda sun kai shekaru 60 da kuma masu shekaru sama da hakan.

A cikin wani rahoto da ta gabatar wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN a ranar Alhamis, NCDC ta bayyana yadda cutar korona take yi wa maza illa fiye da mata.

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, sabbin bayanan alkaluman da NCDC ta fitar sun nuna yadda cutar korona take tasiri a jinsin mutane daban-daban da kuma mutane masu banbancin shekaru a fadin kasar.

Alkaluman da NCDC ta fitar sun nuna cewa:

"An fi samun mutane 'yan shekaru 31 zuwa 40 da suka fi saurin kamuwa da cutar korona."

"Maza mafi yawa a wannan rukunin shekarun sun fi saurin kamuwa da cutar sai dai ba ta fiye kassara su ba"

"A yanzu akwai mutane 797 'yan tsakanin shekaru 31 zuwa 41 duk maza da cutar korona ta harba kuma bakwai daga cikinsu sun halaka."

"Haka kuma akwai mata 324 da ke rukunin wannan shekaru da cutar ta harba, inda hudu tuni sun ce ga garinku nan. Sai dai mace-macen ba su da yawa idan an kwatanta da dattawa.

Shugaban NCDC; Dr. Chikwe Ihekweazu
Shugaban NCDC; Dr. Chikwe Ihekweazu
Asali: Twitter

A cewar rahoton, duk da cewa 'yan shekaru 31 zuwa 40 sun fi saurin kamuwa da cutar, sai dai kuma cutar ta fi sauran hallaka dattawa saboda dalilai na wasu cututtuka na daban da ake samu tattare da su.

KARANTA KUMA: Coronavirus: Aisha Buhari da sauran wadanda suka bayar da gudunmuwa wajen gina babbar cibiyar killace marasa lafiya a Najeriya

Kididdigar alkaluman ta nuna cewa, an fi samun mace-mace a tsakanin mutane 'yan shekaru 61 zuwa 70, duk da cewa kuma su ne ba su fiye saurin kamuwa da cutar ba.

A halin yanzu alkaluman NCDC sun nuna cewa:

"Mutane 'yan shekaru 61 zuwa 70: Maza 188 sun kamu, 3 sun mutu; Mata 2 sun kamu, kuma 4 sun mutu."

"Mutane 'yan shekaru 61 zuwa 70: Maza 188 sun kamu, 3 sun mutu; Mata 52 sun kamu, kuma 4 sun mutu."

"Wadanda suka haura shekaru 70: Maza 74 sun kamu, 12 sun mutu; Mata 33 sun kamu, kuma biyar sun mutu. Hakan ya nuna cewa an fi samun yawan mace-mace wannan rukuni na shekaru."

Haka kuma rahoton ya nuna cewa, an samu yawan mace-mace a tsakanin mutane 'yan shekaru 41 zuwa 50 da kuma 'yan shekaru 51 zuwa 60.

"Mutane 'yan shekaru 41 zuwa 50: Maza 570 sun kamu, 15 sun mutu; Mata 206 sun kamu, kuma hudu sun mutu,"

"Mutane 'yan shekaru 51 zuwa 60: Maza 364 sun kamu kuma 27 sun mutu; Mata 148 sun kamu kuma 3 sun mutu."

A yayin haka kuma, an samu 'yan shekaru 11 zuwa 20 da cutar ta harba kuma uku sun rasa rayukansu. 'Yan kasa da shekaru 10 ba su fiye kamuwa ba sai dai an samu namiji daya da cutar ta hallaka a kasar.

A halin yanzu dai, alkaluman da hukumar NCDC ta fitar a ranar Laraba da daddare sun nuna cewa, akwai mutum 4,971 da cutar korona ta harba kuma 164 sun kwanta dama a duk fadin kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel