COVID-19: Mutum uku sun mutu, wasu sabbin mutum 16 sun kamu a Bauchi

COVID-19: Mutum uku sun mutu, wasu sabbin mutum 16 sun kamu a Bauchi

Gwamnatin Jihar Bauchi ta sanar da cewa wasu sabbin mutum masu cutar korona sun mutu sannan wasu sabbin mutum 16 sun kamu da cutar.

Shugaban Hukumar Inganta Lafiya Bai Daya na Jihar, Dr Rilwani Mohammed ne ya bayyana wa Daily Trust hakan a ranar Alhamis, inda ya kuma ce an sallami mutum 31 ta daka sallama.

Hakan ya kawo adadin wadanda suka kamu da cutar a jihar zuwa 206.

Mohammed wanda kuma shine shugaban kwamitin kar ta kwana na yaki da COVID-19 a jihar ya ce akwai mutum 172 da ke dauke da cutar a cibiyoyin killacewa na jihar.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Allah ya yi wa kwamishina rasuwa a Oyo

Mohammed ya ce, "Mun samu sabbin mutum 16 da suka kamu da cutar a jiya (Laraba), mutum uku sun mutu, an kuma sallami 31 yayin da akwai wadanda ke dauke da cutar 172 a halin yanzu a cibiyoyin killacewa a jihar."

Ya yi kira ga mazauna jihar su cigaba da tsaftace muhallinsu da jikinsu kuma su guji taruwa a wuri guda domin dakile yaduwar cutar a jihar.

Gwamnan jihar, Bala Mohammed a ranar 1O ga watan Mayu ya sanar da dokar kulle a kananan hukumomin Katagum, Giade and Zaki bayan rahotannin mace mace da yaduwar cututtuka a garuruwan.

Sai dai wasu mambobin majalisar jihar Bauchi a ranar Laraba sun yi kira ga gwamnatin jihar ta sake duba dokar kullen ta sassauta ta yadda mutane za su rika yin sallar Juma'a da zuwa majami'u.

Sun bayyana cewa akwai bukatar mutane su tafi wuraren ibada domin su yi addua ga Ubangiji ya taimaki jihar a yakin da ta ke yi da kwayar cutar.

Hakan na zuwa ne bayan an fara samun yawaitar cutar a jihar.

Kamar yadda alkalluman da NCDC ta fitar a daren ranar Laraba, jihar ce ta biyar a jerin wadanda suke kan gaba wurin adadin masu cutar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel