Yanzu-yanzu: An killace Almajirai 2000 a jihar Kano

Yanzu-yanzu: An killace Almajirai 2000 a jihar Kano

Gwamnatin jihar Kano ta sanar da killace daliban makarantun allo da aka fi sani da Almajirai 2000 domin takaita yaduwar cutar Coronavirus a jihar, TheCable ta ruwaito.

Rahoton ya bayyana cewa kwamishanan lafiyan jihar, Aminu Tsanyawa, ya sanar da hakan ranar Alhamis a bikin kaddamar da horon ma'aikatan da za'a daurawa nauyin kula da yaran a cibiyoyin killacewan.

Ya ce wadanda ake horaswa sun hada da Likitoci, ma'aikatan jinya, da masu gwajin da zasu gwada dukkan yaran.

A cewarsa, an ajiye wadannan Almajirai ne a sansanin killacewa uku a kananan hukumomin Kiru, Gabasawa da Karaye.

A yanzu, hukumar hana yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta bayyana cewa jihar Kano ta mutane 707 da suka kamu da cutar ta Coronavirus.

Yayinda aka sallami 79 bayan sun samu lafiya, 33 sun rigamu gidan gaskiya.

Yanzu-yanzu: An killace Almajirai 2000 a jihar Kano
Yanzu-yanzu: An killace Almajirai 2000 a jihar Kano Hoto: Tanko Yakassai
Asali: UGC

KU KARANTA: Mutane 'yan shekaru 31 zuwa 40 sun fi saurin kamuwa da cutar korona - NCDC

A wani labarin mai alaka, Gwamnatin jihar Jigawa ta samu karin mutane 51 da suka kamu da muguwar cutar Coronavirus, 31 cikinsu Almajirai ne da aka turo daga jihar Kano.

Kwamishanan lafiyan jihar, wanda shine shugaban kwamitin yaki da cutar COVID-19, Dakta Abba Zakari, ya tabbatar da hakan ne ga manema labarai a sansanin yan bautar kasa NYSC dake Dutse.

A cewarsa, kashi 56 cikin 100 na masu dauke da cutar Coronavirus a jihar Jigawa Almajirai ne da aka kawo daga jihar Kano.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel