Da duminsa: Gwamnan Gombe ya janye dokar hana Sallar Jam'i, ya ce a bude Masallatai

Da duminsa: Gwamnan Gombe ya janye dokar hana Sallar Jam'i, ya ce a bude Masallatai

Gwamnatin jihar Gombe karkashin jagoranicin gwamna Inuwa Yahaya ta sanar da janye dokar hana ayyukan ibada a jam'i da aka kakaba domin takaita yaduwar cutar Coronavirus a jihar.

Za ku tuna cewa a ranar Laraba, 22 ga Afrilu, gwamnatin jihar Gombe ta kafa dokar hana bude cibiyoyin ibada a fadin jihar domin takaita yaduwar cutar Korona.

Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ya bada umurnin ne na dokar hana fita a kananan hukumomin jihar 11 daga karfe 6 na yamma zuwa na safe.

Amma a yanzu, gwamnan ya ce za'a a iya bude wuraren ibada d sharadin za a yi rika bada tazara da juna.

Ya sanar da hakan ne bayan ganawarsa da shugabannin addinin jihar a gidan gwamnati a ranar Alhamis, 14 ga Mayu, 2020.

Ya ce dokar hana fitan da gwamnatin jihar ta sanya ya baya ta haifi 'da mai ido saboda ya taimaka wajen takaita yaduwar cutar.

A cewarsa, shugabannin addinin sun bada tabbacin cewa za su bi dukkan umurnin da hukumar hana yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta gindaya yayinda bude Masallatai da coci-coci.

Gwamnan ya umurci kwamitin yaki da cutar Koronan jihar ta horar da mamabobin kungiyoyin agajin addinai kan sharruda.

KU KARANTA: Adadin 'yan ta'addan da dakarun Najeriya suka halaka a daren jiya - Rundunar soji

Da duminsa: Gwamnan Gombe ya janye dokar hana Sallar Jam'i, ya ce a bude Masallatai
Da duminsa: Gwamnan Gombe
Asali: Twitter

A bangare guda, Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya amince da dakatar da dokar hana zirga - zirga da kulle jihar Borno sakamakon bullar annobar korona.

Ya janye dokar ne biyo bayan samun gagarumar nasarar da jihar ta yi a bangaren yaki da nnobar korona.

Mataimakin gwamnan Borno, Umar Kadafur, wanda shine shugaban kwamitin kar ta kwana a kan yaki da annobar a jihar, shine yasanar da hakan a cikin wani jawabi da ya fitar a daren ranar Laraba a Maiduguri.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel