Allah ya yi wa mahaifiyar tsohon kwamishinan harkokin cikin gida na Legas rasuwa

Allah ya yi wa mahaifiyar tsohon kwamishinan harkokin cikin gida na Legas rasuwa

Alhaja Risikat Balogun, mahaifiyar tsohon kwamishinan harkokin cikin gida na jihar Legas, Dr Abdul Hakeem Abdul Lateef ta rasu.

Alhaja Risikat Balogun ta shaki numfashin ta na karshe ne a gidan ta da ke Ogba a Legas a ranar Alhamis kamar yadda Afam News ta ruwaito.

Da ya ke bayar da bayani game da rasuwar Alhaja Balogun, hadimin tsohon kwamishinan, AbdulGaniy Oladippupo, ya ce an ki karbar ta a asibitoci masu zaman kansu saboda annobar COVID-19.

Covid-19: Mahaifiyar tsohon kwamishina ta rasu bayan kwana 4 tana jirar sakamakon gwaji

Covid-19: Mahaifiyar tsohon kwamishina ta rasu bayan kwana 4 tana jirar sakamakon gwaji. Hoto daga Afam News
Source: UGC

DUBA WANNAN: Akwai yiwuwar har abada duniya ba za ta rabu da coronavirus ba - WHO

Oladippupo ya ce mahukunta a asibitin sun ki karbar ta na tsawon kwanaki hudu inda suka dage cewa a kai Alhaja Balogun cibiyar killacewa na masu jinyar COVID-19 kafin su duba ta duk da irin mawuyacin halin da ta ke ciki.

Sai dai a lokacin da sakamakon gwajin ta ya fito a ranar Laraba, ya nuna ba ta dauke da kwayar cutar.

"Duk da haka Mama ta rasu a safiyar ranar Alhamis," in ji Oladippupo.

Sanarwar ta Dr. Abdul Lateef, babban limamin masallacin majalisar jihar Legas ya fitar ya ce za a yi wa mahaifiyarsu janaiza a ranar Alhamis bisa koyarwar addinin musulunci.

Dr. Abdul Lateef, tsohon Amirul Hajji na jihar Legas ya yi kira ga alumma kada su damu kansu cewa sai sun hallarci janaizar.

Ya bukaci hakan ne domin biyayya ga umurnin da gwamnati ta bayar na kauracewa cinkoso saboda dakile yaduwar cutar korona da ta zama annoba.

Marigayiya Alhaja Balogun ta rasu ta bar yaya bakwai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Online view pixel