Ana cece-kuce kan wani mangwaro kwaya daya da aka sayar N1,300

Ana cece-kuce kan wani mangwaro kwaya daya da aka sayar N1,300

- Wani dan Najeriya a dandalin sada zumunta, ya sanya hoton wani mangwaro mai tsadar tsiya da janyo mabiyansa suna ta bayyana ra'ayoyin su.

- Mutumin ya sanya hoton mangwaron da aka saye shi N1,300

- 'Yan Najeriya da dama a dandalin sada zumuntar sun sharhi a kan wannan farashi mai ban dariya

Wani mutumin Najeriya mai suna Omo Iya Alamala, ya sanya hoto tare da farashin wani babban mangwaro da ya janyo cece-kuce a dandalin sada zumunta na Twitter.

Wannan lamari ya sanya mabiyan wannan mutumi a dandalin sada zumuntar suka bayyana ra'ayoyinsu daban-daban dangane da farashin 'basamuden' mangwaron.

Alamala ya sanya hoto da farashin mangwaron kwaya daya tilo da aka saye shi a kan Naira dubu daya har da dari uku.

Sai dai fa ya ce babban mangwaron tafiyayye ne kuma dan nan bane, domin kuwa shigo wa aka yi da shi kasar nan.

Farashin wannan mangwaro ya janyo mutane da dama sun bayyana ra'ayoyinsu daban-daban gwargwadon fahimta.

KARANTA KUMA: A ceto tattalin arzikin Najeriya ta hanyoyin da suka dace - Atiku

A yayin da wasu ke mamaki a kan farashin mangwaron, wasu ko sun bayyana takaici yayin da ya zamto abin ban dariya ga wani sashe na mutane.

Ya kara da cewa, a yayin da ake sayar da wannan dan itaciya a wannan farashi mai girma, sai dai kuma ga mangwaro nan kamar banza saboda tsabar yalwarsa a wurare irin su Benuwe da Ogbomoso da ke Najeriya.

Babu shakka farashin wannan mangwaro ya fusata matashi Alamala, kamar yadda bincike ya nuna.

A wani bangare na daban, mahukuntan lafiya sun tabbatar da cewa, mangwaro na daya daga cikin kayan itatuwa masu tarin albarka ta bunkasa garkuwar jiki da ya kamata mutane su dage wajen shan sa.

Babu shakka a wannan lokaci da annobar korona ta yi wa duniya lullubi, ingatacciyar garkuwar jiki ita kadai ce riga-kafin da za ta rufa wa mutum asiri ganin yadda har kawo yanzu ba a samu maganin cutar ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel