Tsohon layin wayar diyar Buhari: Kotu ta ci tarar DSS miliyan N10

Tsohon layin wayar diyar Buhari: Kotu ta ci tarar DSS miliyan N10

Wata kotun tarayya da ke zamanta a Asaba, babban birnin jihar Delta, ta ci tarar hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) miliyan goma a kan tsare wani matashi, Anthony Okolie, na tsawon sati goma ba bisa ka'ida ba.

A shekarar 2019 ne hukumar DSS ta kama matashin Okolie bayan ya cigaba da amfani da wani layin waya da diyar Buhari, Hanan, ta taba amfani da shi.

Duk da matashin ya gabatar da shaidar sayen layin bisa ka'ida, hukumar DSS ta tsare shi bisa zargin yana amfani da layin wajen mu'amala da mutane da sunan Hanan. Zargin da Okolie ya musanta.

A cikin watan Fabrairu ne Legit.ng ta wallafa labarin cewa jami'an hukumar tsaro na farin kaya (DSS) sun kama tare da tsare wani matashi, Anthony Okolie, sakamakon ya sayi wani layin waya na kamfanin sadarwa, MTN, da diyar Buhari, Hanan, ta taba amfani da shi a baya.

Okolie ya sayi layin wayar ne tun a shekarar 2018, shekaru biyu kafin kamun da jami'an tsaro suka yi masa.

An kama shi ne ranar Litinin, 22 ga watan Yuli, 2019.

Jami'an DSS sun yi awon gaba da Okolie zuwa Abuja kafin daga bisani ya shaki iskar 'yanci a watan Disamba, 2019.

Tsohon layin wayar diyar Buhari: Kotu ta ci tarar DSS miliyan N10

Tsohon layin wayar diyar Buhari: Kotu ta ci tarar DSS miliyan N10 Hoto: SaharaReporters
Source: UGC

Tope Akinyode, lauyan Okolie, ya ce hukumar DSS ta tsare matashin na tsawon makonni 15.

Akinyode, ya bayyana cewa kamfani ne ya sake dawo da layin wayar kasuwa bayan Hanan ta daina amfani da shi.

DUBA WANNAN: Zulum ya janye dokar kulle jihar Borno, ya umarci a bude Masallatai

"Ya sayi layin wayar ne bisa ka'ida ba tare da sanin waye ya yi amfani da shi ba a baya," a cewar Akinyode.

Lauyan ya kara da cewa an saba ka'ida wajen kama Okolie tare da tsare shi a kan layin da ya saya kuma aka bashi takardar shaidar cinikayya (Receipt).

Sai dai, Hanan ta musanta zarginta da ake da cewa ta umarci jami’an tsaron farin kaya na DSS da su damke Okolie a kan amfani da layin wayar da ta taba amfani da shi.

Okolie ya maka hukumar tsaro ta farin kaya a kan take masa hakkinsa da suka yi ta hanyar garkame shi na sama da makwanni 15.

Ya hada da Hanan Buhari tare da MTN a cikin wadanda yake kara tare da bukatar diyyar naira miliyan 500 na take masa hakkinsa da aka yi.

Kamar yadda Okolie ya bayyana a gaban babbar kotun tarayya da ke Asaba, yace ya siya layin wayar ne a kan naira dubu daya a ranar 8 ga watan Disamba 2018, a kasuwar Ogbeogonogo da ke kan titin Nebu a jihar Delta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel