Masha Allah: Karamar yarinya yar shekara 6 ta warke daga cutar Coronavirus a Jigawa

Masha Allah: Karamar yarinya yar shekara 6 ta warke daga cutar Coronavirus a Jigawa

Wata karamar yarinya yar shekara 6 ta rabu da cutar Coronavirus mai toshe numfashi a jahar Jigawa.

Yarinyar, yar asalin garin Kazaure an sallameta daga cibiyar killace masu cutar Coronavirus dake garin Dutse ne tare da mahaifinta, wanda daga wajensa ta samu cutar.

KU KARANTA: Mataimakin shugaban jam’iyyar APC da diyarsa sun fada hannun barayin mutane a Kaduna

Rahoton gidan talabijin na Channels ta bayyana cewa mahaifin yarinyar ya yi tafiya zuwa jahar Enugu ne, inda dawowarsa gida Kazaure aka gane yana dauke da cutar.

Kuma wannan mutumi shi ne na farko da ya fara kamuwa da cutar a garin Kazaure gaba daya, kamar yadda kwamishinan jahar kiwon lafiya na jahar, Abba Zakari ya bayyana.

Masha Allah: Karamar yarinya ya shekara 6 ta warke daga cutar Coronavirus a Jigawa
Jigawa Hoto: Channels
Asali: UGC

Idan za’a tuna, kwanaki 8 da suka gabata ne aka dauke yarinyar daga gidansu a Kazaure zuwa garin Dutse domin samun kulawa bayan gwajin da aka mata ya nuna tana dauke da cutar.

Daga cikin mutane 18 da suka yi mu’amala da mahaifinta, kuma aka gudanar da gwajin cutar a kansu, ita kadai ce sakamakon gwajin ya tabbatar ta kamu da cutar.

Kwamishinan ya kara da cewa baya ga yarinyar yar shekara 6 da mahaifinta, jahar Jigawa ta sallami wasu mutane biyar da suka warke daga cutar Coronavirus.

Bugu da kari akwai wasu mutane 20 da a yanzu sakamakon gwaji ya nuna sun rabu da cutar, amma ba za’a sallame suba har sai an kara gudanar da gwaji na biyu a kan su don a tabbatar.

Abba yace suna baiwa marasa lafiya magungunan da suka hada da hydroxycholoroquine da Azithromycin, kuma hakansu ta cimma ruwa saboda magungunan sun yi amfani.

Akwai mutane 118 da suka kamu da cutar Coronavirus a jahar Jigawa, mutane 63 daga cikinsu almajirai ne da aka mayar da su gida daga jahar Kano.

A wani labarin kuma, Majalisar koli ta shariar Musulunci, NSCIA, ta yi kira ga Musulmai su gudanar da addu’o’i a ranar Alhamis don neman taimakon Allah game da annobar Coronavirus.

Majalisar ta shirya wannan addu’o’i ne tare da hadin gwiwar kungiyar Musulmai a Najeriya, biyo bayan gabatar da bukatar hakan da wata kungiyar addinai ta duniya ta yi.

Shuwagabannin kungiyar mai suna Supreme Committee for Human Fraternity da suka hada da Sheikh Al-Azhar Al-Sharif da shugaban kiristocin Katolika Paparoma Francis ne suka yi kiran.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel