Yanzu-yanzu: Allah ya yi wa kwamishina rasuwa a Oyo
Kwamishinan Muhalli da Albarkatun kasa na jihar Oyo, Mr Kehinde Ayoola ya rasu.
Ya rasu yana da shekaru 55 a duniya.
Ayoola, tsohon kakakin majalisar jihar ta Oyo, ya yi fama da rashin lafiya na kimanin sati biyu.
Ya rasu ne a wani asibiti mai zaman kansa a Iyaganku a garin Ibadan inda ake masa magani.
Dan siyasan haifafar garin Oyo ya wakilci mazabar Oyo ta Gabas daga shekarar 1999 and 2003.

Asali: UGC
DUBA WANNAN: Buhari ya nada sabon shugaban NALDA
An haifi Ayoola ne a ranar 14 ga watan Janairu a garin Oyo na jihar Oyo.
Ya yi karatun digir a Jamiar Obafemi Awolowo da ke Ile Ife.
Ya yi karatun nazarin kimiyyar dabobi da kula da muhalli.
Ya auri Olukemi, mataimakiyar Farfesa a tsangayar nazarin aikin noma.
Kuma suna da yara biyu.
Taiwo Adisa, mai magana da yawun gwamnan jihar Oyo Rotimi Makinde shima ya tabbatar da rasuwar kwamishinan.
Ba a tabbatar da cutar da ta yi sanadin rasuwarsa ba a lokacin hada wannan rahoton kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng