A ceto tattalin arzikin Najeriya ta hanyoyin da suka dace - Atiku

A ceto tattalin arzikin Najeriya ta hanyoyin da suka dace - Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, ya ce kwaskwarimar da aka yiwa kasafin kudin Najeriya na 2020 ba ta da wani muhimmanci wajen ceto tattalin arzikin kasar.

Atiku ya ce gyaran da aka yiwa kasafin kudin bana na rage Naira biliyan 71 daga cikinsa ba zai yi wani tasirin gaske ba wajen tsamo tattalin arzikin kasar nan daga halin da ya ke ciki a yanzu.

A zaman majalisar zartarwa da aka gudanar a ranar Laraba, wanda shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta, an shigar da kwaskwarimar da aka yi wa kasafin kudin kasar cikin doka.

Majalisar ta amince da ragin da aka yiwa kasafin kudin bana daga Naira tiriliyan 10.594 zuwa Naira tiriliyan 10.523, wanda ya nuna banbancin Naira biliyan 71 kenan.

Ministar kudi, kasafi da tsare-tsare a kasar, Zainab Ahmed, yayin ganawa da manema labarai na fadar shugaban kasa bayan zaman majalisar ta fadi dalilin wannan hukunci da aka yanke.

Ta ce an shigar da wasu sabbin tsare-tsare cikin kwaskwarimar da aka yiwa kasafin kudin na bana domin tunkarar tasirin da annobar korona za ta yiwa tattalin arzikin kasar.

Sai dai da ya ke martani kan hukuncin da majalisar ta zartar, tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce babu wani banbanci na a-zo-a-gani a kasafin kudin da kuma kwaskwarimar da ka yi masa a yanzu.

Buhari da Atiku

Buhari da Atiku
Source: UGC

Ya bayyana mamakin yadda har yanzu gwamnatin Buhari ta zabi holewa a lokacin da ake da matsananciyar bukata ta ceto tattalin arzikin kasar.

Cikin wani sako da tsohon mataimakin shugaban kasar ya wallafa a ranar Alhamis kan shafinsa na Facebook, ya shawarci shugaba Buhari a kan mafi kyawun hanyoyin da za a bi don shawo kan mummunan yanayin da annobar korona ta jefa tattalin arzikin kasar.

A sakon mai taken "bai dace Najeriya ta fifita walwala ba a lokacin bukata", Atiku ya nemi Buhari ya yi watsi da kasafin Naira biliyan 37 da aka kudirta kashewa wajen gyaran majalisun dokoki na tarayya.

Ya yi roko a kan rage manyan kasafin kudade da aka kudirta batar wa wajen gudanar da al'amura a majalisun tarayya da kuma fadar shugaban kasa.

KARANTA KUMA: Yadda jami'an tsaro ke sabawa dokar hana zirga-zirga

Atiku wanda ya yi takarar shugaban kasa a babbar jam’iyyar adawa ta PDP yayin babban zabe a shekarar 2019, ya nemi Buhari ya jingine biliyoyin kasafin kudin tafiye-tafiye da na ciyarwa da aka ware musu shi da mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya kuma ba da shawarar a yi watsi da kasafin kudin sayen motocin alfarma ga shugaban kasar da mataimakinsa da kuma sauran masu rike da mukaman siyasa.

Ya kuma nemi Buhari ya sayar da 8 ko 9 daga cikin jiragen sama na fadar shugaban kasa tare da rage albashin wadanda aka yi wa nadin mukamai na siyasa.

Sai dai Wazirin na Adamawa ya gargadi gwamnatin Buhari a kan kada ta kuskura ta taba albashin ma'aikatan gwamnati.

Ya ke cewa: "A lokacin da ake da bukata mai giraman gaske, babu wata al'umma, ko kasar mai karamin tattalin arzikin irin na mu, da ya kamata ta masu rike da madafan iko su kasance cikin walwala da holewa."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel