Satar shanu: Kansilar da ake nema ruwa a jallo ya shiga hannu
Wakana Enan Ngari, Kansilar da ake nema ruwa a jallo a kan zargin satar shanu da wasu laifufuka a jihar Adamawa ya mika kansa hannun Yan sanda a karamar hukumar Numan na jihar.
DSP Suleiman Nguroje, Mai magana da yawun rundunar yan sanda na Adamawa ne ya bayyana wa manema labarai hakan a ranar Alhamis a Yola kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Nguroje ya ce an tafi da kansilar da ake zargi zuwa sashin binciken manyan laifuka na rundunar (CID) domin cigaba da bincike.

Asali: UGC
DUBA WANNAN: Akwai yiwuwar har abada duniya ba za ta rabu da coronavirus ba - WHO
Nguroje ya ce, "Rundunar yan sandan jihar Adamawa tana son sanar da alumma cewa Kansila mai wakiltan mazabar Vulpi a karamar hukumar Numan ya mika kansa ga yan sanda.
"A baya gwamnatin jihar Adamawa ta fitar da sanarwar neman kansilar ruwa a jallo sakamakon zargin da ake yi na cewa yana da hannu wurin aikata wasu laifuka.
"Ya mika kansa ga Yan sanda a Numan kuma tuni an mika shi ga sashin binciken manyan laifuka (CID) domin bincike."
Kakakin yan sandan ya kuma ce ya jiyo kwamishinan yan sandan jihar, Mr Olugbenga Adeyanju yana kira ga alummar jihar musamman na Numan su kwantar da hankulansu su zauna lafiya.
Ya ce shugaban yan sandan ya bayar da tabbacin za a gudanar da bincike a kan wanda ake zargin kuma idan an same shi da laifi, rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba har sai an hukunta shi.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng