Tsaro: Na shirya ba rayuka da dukiyoyin 'yan kasa kariya - Buhari (Hotuna)

Tsaro: Na shirya ba rayuka da dukiyoyin 'yan kasa kariya - Buhari (Hotuna)

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi taron da shugabannin tsaron kasar nan tare da wasu manya a fannin tsaron kasar nan

- Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, sakataren gwamnatin tarayya, babban mai bada shawara a fannin tsaron kasa duk sun samu halarta

- Ministan shari'a kuma Antoni janar din tarayya, ministan harkokin waje da kuma ministan tsaro, Bashir Magashi duk sun hallara

A yau Alhamis, 14 ga watan Mayun 2020, shugaba Buhari ya shiga ganawar sirri da shugabannin tsaron kasar nan a Abuja, babban birnin tarayyar kasar nan.

An fara taron babu jimawa da isar shugabannin tsaron fadar shugaban kasar da ke Aso Villa, a babban birnin tarayyar.

Tsaro: Na shirya ba rayuka da dukiyoyin 'yan kasa kariya - Buhari
Tsaro: Na shirya ba rayuka da dukiyoyin 'yan kasa kariya - Buhari. Hoto daga Channels TV
Asali: Twitter

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar wa da 'yan kasar Najeriya cewa ya shirya tsare musu rayukansu da kadarorinsu.

Ya bada wannan tabbacin ne a taron da yayi da Shugabannin tsaron kasar nan a yau Alhamis a fadar shugaban kasa da ke Aso Villa.

Tsaro: Na shirya ba rayuka da dukiyoyin 'yan kasa kariya - Buhari
Tsaro: Na shirya ba rayuka da dukiyoyin 'yan kasa kariya - Buhari. Hoto daga Channels TV
Asali: Twitter

Mai bada shawara a kan tsaron kasa, Babagana Monguno, ya bayyana matsayar shugaban kasar a yayin da yake bayani ga manema labaran gidan gwamnati a karshen taron.

Ya ce, ya yi bayani ga taron wanda ya kunshi sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, a kan halin da kasar nan take ciki na barkewar annobar Coronavirus.

Tsaro: Na shirya ba rayuka da dukiyoyin 'yan kasa kariya - Buhari
Tsaro: Na shirya ba rayuka da dukiyoyin 'yan kasa kariya - Buhari. Hoto daga Channels TV
Asali: Twitter

Taron ya samu halartar mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, shugabannin cibiyoyin tsaro da wasu ministoci.

Ministocin sun hada da ministan tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi mai murabus; Ministan shari'a kuma Antoni Janar din tarayya, Abubakar Malami; da kuma Ministan harkokin waje Geoffrey Onyeama da sauransu.

Tsaro: Na shirya ba rayuka da dukiyoyin 'yan kasa kariya - Buhari
Tsaro: Na shirya ba rayuka da dukiyoyin 'yan kasa kariya - Buhari. Hoto daga Channels TV
Asali: UGC

Shugabannin tsaron sun samu jagorar Janar Abayomi Olonisakin.

Shugaban rundunar sojin sama, Air Marshal Sadique Abubakar, shugaban rundunar sojin ruwa, Ibok Ekwe Ibas da shugaban tsari na sojin kasa, Laftanal Janar Lamidi Adeosun.

Tsaro: Na shirya ba rayuka da dukiyoyin 'yan kasa kariya - Buhari
Tsaro: Na shirya ba rayuka da dukiyoyin 'yan kasa kariya - Buhari. Hoto daga Channels TV
Asali: Twitter

Sauran sun hada da sifeta janar din 'yan sanda, Mohammed Adamu da darakta janar din jami'an tsaron farin kaya, Yusuf Bichi.

Yanzu-yanzu: Buhari ya shiga ganawar gaggawa da shugabannin tsaro
Yanzu-yanzu: Buhari ya shiga ganawar gaggawa da shugabannin tsaro. Hoton daga Channels TV
Asali: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel