COVID-19: Hydroxychloroquine na sha na warke daga korona - Doyin Okupe

COVID-19: Hydroxychloroquine na sha na warke daga korona - Doyin Okupe

Doyin Okupe, tsohon mai magana da yawun tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, ya ce “hydroxychloroquine” na daga cikin magungunan da aka ba shi ya sha har ya warke daga cutar korona.

The Punch ta ruwaito cewa an sallamo Okupe da matarsa, Aduralere bayan sun kwashe sati biyu a cibiyar killace majinyata da ke garin Sagamu a jihar Ogun.

Ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa a ranar Talata cewa, "A ranar 23 na watan Afrilu, ni da matata Aduralere mun kamu da COVID-19. Cikin ikon Allah, an sallamo mu a safiyar 12 ga watan Mayu bayan gwaji ya nuna mun warke. Ina gode wa Allah saboda jin kansa."

DUBA WANNAN: Satar Shanu: Ana neman kansila ruwa a jallo

Daga baya a daren ranar Laraba ya bayyana magungunan da aka bashi duk da cewa ya ce har yanzu masana kimiyya ba su cimma matsauya ba a kan takamamen maganin na cutar korona.

"Magungunan COVID-19. Hydroxychloroquine 400mg na sau biyu a rana na kwanaki biyu, sai 400mg sau daya na kwanaki uku. Azithromycin 500mg fly Zinc Sulphate 100mg sau daya a kullum. VitzC 1200mg sau daya kullum.

"Ina kuma yin kari da citta, tafarnuwa da kurkur da lemun tsami. A Kaduna suna ba wa majinyata ganyen Dogonyaro."

"Babu takamammen magunguna da likitoci ko masana kimiyya suka cimma matsaya a kai. Babu wani ingantaccen binciken masana da ke nuna yadda ake magance COVID-19. Abinda ya fi muhimmanci shine karfin garkuwar jikin masu jinyar."

"Idan ya zama dole ka sha hydroxychloroquine, ta tuntubi likitan ka ya tabbatar ba ka matsalar zuciya. Idan kana da shi, kana bukatar kulawa ta musamman kafin amfani da wannan magungunan.

"Kashi 90 to 95 cikin majinyata su kan warke ma ba tare da an kwantar da su a asibiti ba. Kashi 90 na matasa za su warke ko da sun kamu, " kamar yadda Okupe ya bayyana a Twitter.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel