Yadda jami'an tsaro ke sabawa dokar hana zirga-zirga

Yadda jami'an tsaro ke sabawa dokar hana zirga-zirga

Masu motocin haya da sauran masu zirga-zirga a ababen hawa su na ci gaba da shige-da-ficensu a tsakanin jihohin Najeriya duk da an sanya dokar hana zirga-zirga a yunkurin dakile yaduwar cutar korona a kasar.

Yayin da wasu direbobi tuni sun tsawwala wa fasinjoji ta hanyar ninka kudin haya domin sayen hanya a wuraren da jami'an tsaro suka sanya shinge kan tituna, wasu kuwa sun kirkiri hanyoyi na daban a cikin dokar daji domin biyan bukatar fasinjojin da su ka dauko.

Binciken jaridar Daily Trust ya nuna cewa, wannan lamari yana dugunzuma al'umma saboda hatsari ne da zai haddasa ci gaba da yaduwar cutar a jihohin kasar.

Tun daga ranar 4 ga watan Mayu, wadda ita ce ranar da dokar hana zirga-zirga tsakanin jihohi ta fara aiki, akwai mutum 2, 802 masu cutar korona a Najeriya.

Sai dai kuma tun daga wancan lokaci ya zuwa ranar Talata, 12 ga watan Mayun, adadin masu cutar ya karu zuwa 4, 641 a fadin kasar.

Wannan shi ya ke nuna an samu karin adadin masu cutar da kaso 60 cikin 100 a tsakanin kwanaki takwas kacal.

Baya ga umarnin gwamnatin tarayya na hana zirga-zirga tsakanin jihohi, gwamnonin jihohi 36 na Najeriya sun amince da a tabbatar da wannan doka har tsawon makonnin biyu.

Duk da an garkame tashoshi, amma har yanzu ana zirga-zirga tsakanin jihohi.

Manema labarai a Kano sun gano wani sabon salo na sabawa dokar hana zirga-zirga tsakanin jihohi, inda matafiya ke sauka daga motoci a kan iyakar sannan su bi ta barauniyar a kan babura ba tare da an lura da su.

Wasu daga cikin wadannan matafiya da suka hadar har da 'yan Nijar, su kan yi basaja a matsayin 'yan kasa wajen yin zirga-zirga a manyan hanyoyi zuwa kowane sassa na jiha a kan babura domin gudanar da harkokinsu na kasuwanci.

Bincike ya nuna cewa matafiya daga Zariya su kan sauka a Kwana Dangora sannan su hau babura da zai ketare da su zuwa Kura, inda daga nan kuma su sake hawa wasu motocin da za su kawo su cikin birnin Kano.

Masu shigowa da jihar Katsina kuma, su kan sauka ne a garin Yankamai da ke karamar hukumar Tsanyawa, inda daga nan su kutso cikin birnin Dabo domin cin kasuwa.

Kwamishinan 'yan sanda na jihar Kano, Habu A. Sani, ya ce an gano dukkan iyakokin da ke kananan hukumomi tara na jihar domin aiwatar da dokar hana zirga-zirga tsakanin jihohin.

Sanarwar babban jami'in ta zo yayin ganawa da manema labarai a fadar gwamnatin Kano bayan da dokar kulle da shugaba Muhammadu Buhari ya sanya ta fara aiki a jihar.

Duk da cewa kakakin 'yan sandan jihar DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ba zai iya tabbatar da adadin mutanen da ya zuwa yanzu aka kama da laifin sabawa dokar ba, sai dai ya ce an kama mutane masu tarin yawa.

Yayin da dokar hana zirga-zirga ta fara aiki a Najeriya

Yayin da dokar hana zirga-zirga ta fara aiki a Najeriya
Source: Original

A jihar Neja kuma, matakin keta wannan doka ya kai wani munzali, yayin da kwamitin kula da yaduwar cutar a jihar ya tabbatar da cewa har yanzu ana ci gaba da kama masu sabawa dokar.

Shaidar sabawa dokar ta tabbata a fili yayin da mutanen da a kwanan nan aka gano suna dauke da kwayoyin cutar korona suka kasance matafiya da suka kutso jihar daga Legas da kuma Kano.

Lamarin da ya sanya gwamnan jihar ya ce 'yan kasuwa da kuma saura matafiya masu shigowa daga jihar Kano za a rika killace su har na tsawon makonni biyu bayan dawowar su.

KARANTA KUMA: Jihohi 35 a Najeriya wanda coronavirus ta bulla - NCDC

Yayin da idanu suka leka iyakar Jos da Bauchi da ke Sabon Gari Narabi, motoci da dama sun yi dako a gabar shingen da jami'an tsaro suka sanya a kan hanya.

A bangare daya kuma matasan gari tare da hadin gwiwar jami'an tsaro 'yan sa-kai, sun samar wa motocin haramtattun hanyoyi inda su ma suka bude cin kasuwa.

Matasan da suka yi wa direbobin hanya ta cikin dokar daji su na karbar akalla N300 duk mota guda.

Da ya ke magana a kan lamarin, kwamishinan 'yan sanda na Bauchi, CP Philip Maku, ya ce sun gano haramtattun hanyoyi 12 da matafiyan ke sabawa dokar hana zirga-zirga, kuma tuni suka dode su.

Wani direban mota a Jos da ya fadi cewa sunansa Mallam, ya ce kusan kullum sai ya je Kano ya dawo abin sa dauke da fasinjoji.

Sai dai ya ce yana biyan masu tsaron hanyar ne inda ya ke fanshewa ta hanyar tsawwala farashin kudin hayar motarsa a kan fasinjoji.

Ya kuma ce akwai jami'an tsaro masu wuyar sha'ani da dole a wasu lokutan sai dai ya yi sha-tale-talen hanya ta cikin dokar daji.

A jihar Taraba kuma, bincike ya nuna cewa matukar dare ya raba, to kuwa jami'an tsaro sun budewa direbobi hanya amma fa a kan farashi daga N5, 000 har zuwa N10, 000 ga duk mota daya.

Irin wannan sabawa doka na ci gaba da kasancewa a wasu jihohin kasar nan da mashaida suka tabbatar kamar Kaduna, Nasarawa, Benuwe, Borno, da kuma Osun.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel