Sabon sautin murya: Muhimman sakonni 5 da Shekau ya fitar

Sabon sautin murya: Muhimman sakonni 5 da Shekau ya fitar

Shugaban Jama'atu Ahlussunnah Lidda'awati Wal Jihad, Abubakar Shekau, ya saki sabon sakon murya inda ya bayyana cewa tsohon sautin muryarsa ne ake yadawa na shekaru biyar da suka gabata.

A sautin muryar mai tsawon mintoci 24 da dakika 56, shugaban 'yan ta'addan ya ce wurin Allah yake neman dauki ba wajen kowa ba.

Don nuna sabon sautin murya ne, ya fara da bayyana sunansa, kwanan wata da kuma tsohon sautin muryar.

Kamar yadda yace, "Ina son mika sako ga wadanda suka yi amfani da muryarmu suka yi mana karya. Duk wanda ya dauka muryar wani don tozarta shi, wallahi ba zai yi nasarar ba," Shekau yace.

"Wannan tsohon sautin murya ne wanda na fitar a shekaru biyar da suka gabata a watan azumi. Addu'a ce nake yi ta neman tallafin Ubangiji.

"Ko a yanzu, ba zan sassauta irin kalaman nan ba na neman taimakon Allah," yace.

KU KARANTA KUMA: Kannywood: Allah ya yi wa tsohon jarumi, Daudu Galadanci rasuwa

Bayan nan Shekau ya bada wasu sakonni ga wadanda lamarin ya shafa tare da jan musu kunne. Ga sakonni da ya fitar a sakon sautin muryar:

1. Barazana ga manema labarai da 'yan jaridu

Shekau ya yi barazana ga lauyan nan mai zama a London kuma mai bincike, Audu Bulama Bukarti, Editan jaridar HumAngle, Ahmad Salkida da BBC.

Ya zargesu da yada labarai wanda a cewarsa halayyar yahudawa ce.

A cewarsa, Bukarti na cikin babbar matsala duk da kuwa ba a Najeriya yake ba don yana sukar jihadi. Ya bayyana cewa, tuni sun san Salkida kuma ya kiyaye tun kafin su je kansa.

Ya zargesu da sukar addinin Allah.

2. Mu ba masu rauni bane

Duk da raunin kungiyar da ya bayyana a tsohon sautin muryar, Shekau ya ce har yanzu kungiyarsa na nan daram. Rundunar sojin Najeriya bata isa ta firgita su ba.

3. Ku yi watsi da dokar nesa-nesa da juna don dakile yaduwar cutar coronavirus

Shekau ya ce cutar korona fushin Allah ce a kan kowa. Suna sallolinsu biyar a jam'i tare da sallar Juma'a.

4. Ya sake jaddada manufar Boko Haram

A sabon sautin muryar, Shekau ya ce karanta wani fannin ilimi da ba na Musulunci ha haramub ne kuma bacin lokaci ne.

Ya yi kira ga jama'a da su yi watsi da kimiyya, fasaha, sanin halayyar dan Adam da sauransu.

5. Ya caccakin shugabannin Afrika

Shekau ya caccaki shugabannin Afrika wadanda suka takura mayakan Boko Haram a yankin yammacin Afrika. Ya yi kira ga shugabannin kasar Chadi, Nijar, Kamaru da Najeriya.

Ya ce babu wata nasara da za su samu a kan masu daukaka kalmar Allah.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel