Sarkin Musulmi ya umarci Musulmai su yi addu’o’in ganin bayan Corona a ranar Alhamis
Majalisar koli ta shariar Musulunci a Najeriya, NSCIA, ta yi kira ga Musulmai su gudanar da addu’o’i a ranar Alhamis don neman taimakon Allah game da annobar Coronavirus.
Punch ta ruwaito majalisar ta shirya addu’o’in ne tare da hadin gwiwar kungiyar Musulmai a Najeriya, biyo bayan gabatar da bukatar hakan da wata kungiyar addinai ta duniya ta yi.
KU KARANTA: Majalisar zartarwa ta ware N47bn don inganta lantarki a yankin Arewa maso gabas
Shuwagabannin kungiyar mai suna Supreme Committee for Human Fraternity da suka hada da Sheikh Al-Azhar Al-Sharif da shugaban kiristoci Paparoma Francis ne suka yi wannan kira.
Shuwagabannin sun nemi dukkanin kungiyoyin addinai dake duniya su gudanar da addu’o’in ganin karshen annobar Coronavirus tare da duk matsalolin da ya sabbaba.
Wata sanarwar da shugaban kwamitin Fatawa na NSCIA, Sheikh Shariff Ibrahim Saleh ya fitar a ranar Laraba ta bayyana cewa sakataren majalisar dinkin duniya ya goyi bayan addu’o’in.
Sheikh Saleh yace baya ga sakataren UN, Antonio Gutteres, sauran manyan maluman addinin Musulunci na duniya ma sun amince a gudanar da addu’o’in.

Asali: UGC
“Duba da ayoyin Qur’ani, tare da bin tafarkin Manzon tsira, an nemi mu yi zikiri da addu’o’I ga Allah a irin wannan lokaci na masifa, a madadin kwamitin Fatawa na NSCIA, da kuma shawarar shugaban NSCIA mai alfarma Sarkin Musulmi, a madadin kungiyar AMIN,
“Muna kira ga Musulmai da Kiristocin Najeriya su yi addu’o’i sosai da sosai a duk inda suke da murya daya a ranar 14 ga watan Mayu don Allah Ya kawo mana karshen wannan annoba.
“Sunnan Annabi ya nuna ana shawartar mutane su fita yayin da ake ruwan sama su yi addu’a. sa’annan muna kira ga shuwagabannin addinai a kasa da duniya gaba daya su cigaba da aiki tukuru don ganin an samu hadin kai da zaman lafiya a ko ina.”Inji shi.
A wani labari kuma, Kasar Saudi Arabia ta lissafa yan Najeriya 11,600 da suke makale a cikin kasarta saboda annobar Coronavirus, kuma ta fara shirin mayar dasu gida Najeriya.
Wani jami’in ofishin jakadancin Najeriya da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa Saudiyya ta sanar da su wannan matakin tun makonni da suka gabata.
A cewar Saudiyya, akwai yan Najeriya da suka tafi a Umrah amma saboda Corona basu samu daman komawa gida ba sakamakon matakan da gwamnatin kasar ta dauka.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng