Yadda wani mutum ya zazzabga wa 'yar sanda mari

Yadda wani mutum ya zazzabga wa 'yar sanda mari

Wata kotun tafi da gidanka da ke yankin Gudu ta yanke wa wani mutum mai suna Sunday Okafor hukuncin wata daya a gida yari ba tare da tara ba.

An kama Okafor da laifin zabga wa 'yar sanda mari a farfajiyar kotu.

Okafor ya hada da cin zarafin wata ma'aikaciyar hukumar gidan yarin. Ya bankade ta har ta fadi kasa a yayin wata muhawara a farfajiyar kotun.

Alkalin mai shari'a, Abdulrazak Musa Eneye wanda ya ga lokacin da mutumin ke cin zarafin ya yanke hukunci.

Mutumin da ya fadi kasa yana kuka tare da rokon rangwame, an tasa keyarsa zuwa gidan gyaran hali da ke Kuje don ya kwashe wa'adin daurinsa.

Yadda wani mutum ya zazzabga wa 'yar sanda mari
Yadda wani mutum ya zazzabga wa 'yar sanda mari. Hoto daga The Nation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Atiku da Saraki sun yi martani a kan nadin Farfesa Gambari

A wani labari na daban, wata kotun majistare da ke zama a Kano ta bada umarnin damko Malam Kabiru Ado-Panshekara, shugaban karamar hukumar Kumbotso da ke jihar a kan kin bayyana a gaban kotu.

Alkalin kotun majistaren, Musa Ibrahim ya bada damar kamo wanda ake zargin don ya gurfana a gaban kotu sakamakon zarginsa da ake da cin amana.

Mai gurfanarwa, Salisu Tahir, ya sanar da kotun cewa a ranar 9 ga watan Mayun 2020, wanda ake zargi kuma shugaban karamar hukumar Kumbotso, an damka masa fom na raba tallafin rage radadi.

"Wanda ake zargin ya waskar da wasu fom din inda ya bai wa wasu wadanda basu cancanta ba," yace.

Tahir ya yi kira ga kotun da ta bada damar damko wanda ake zargin saboda ya ki zuwa kotun koda aka aika masa da sammaci.

Ya ce laifinsa ya ci karo da sashi na 315 na dokokin Penal Code da kuma sashi na 26 na dokokin rashawa na 2008, kamar yadda jaridar The Nation ta wallafa.

Lauyan wanda ke kare kansa, Ibrahim Adamu, ya sanar da kotun cewa bai san dalilin da ya hana wanda ake zargin gurfana a gaban kotun ba.

"Daya daga cikin hadiman Ado Panshekara ya sanar da ni cewa yana kan hanyar zuwa kotun," yace.

Adamu ya roki kotun da ta kara wa wanda ake zargin mintocin 30 don ya samu isowa. Kotun ta dage zamanta zuwa ranar 27 ga watan Mayu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel