COVID-19: Tsohuwa mai shekaru 98 da warke daga korona a Legas

COVID-19: Tsohuwa mai shekaru 98 da warke daga korona a Legas

An sallami wata tsohuwa mai shekaru 98 da haihuwa daga cibiyar killace masu dauke da cutar COVID-19 a Legas bayan ta warke sarai.

Babajide Sanwo Olu, gwamnan jihar Legas ne ya sanar da hakan ta shafin Twitter a daren ranar Laraba.

Tana daya daga cikin mutane 26 da aka sallama a jihar ta Legas a ranar Laraba bayan an musu gwaji kuma sakamakon ya nuna sun warke.

DUBA WANNAN: COVID-19: Saudiyya za ta saka dokar kulle yayin hutun sallar Idi mai zuwa

Sakon da gwamnan ya wallafa a Twitter ya ce, "Yau, mun sallami wata tsohuwa mai shekaru 98, ita ce mai jinya mafi shekaru da muke da ita a Legas.

"An sallame ta tare da wasu majinyata 25, 13 maza yayin da 12 mata bayan gwajin da aka yi musu ya nuna sun warke daga cutar ta #COVID19, hakan ya kawo jimillar wadanda suka warke zuwa 528."

Sanwo Olu ya kuma mika godiyarsa ga maaikatan lafiya da sauran maaikatan da ke kan gaba wurin yaki da annobar a jihar.

Ya kuma yi kira da mutanen jihar su cigaba da kiyayye sharrudan da hukuma ke bayarwa domin kare kansu daga mummunar cutar.

A zuwa ranar 12 ga watan Mayun 2020, an tabbatar mutum 1,990 masu dauke da COVID-19 a jihar ta Legas adadin da ya dara na kowanne jiha a kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel