Tinubu ya yi tsokaci game da nadin da Buhari ya yi ma Ibrahim Gambari

Tinubu ya yi tsokaci game da nadin da Buhari ya yi ma Ibrahim Gambari

Jagoran APC, Asiwaju Ahmed Bola Tinubu ya jinjina ma shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa nadin da ya ma Farfesa Ibrahim Gambari a matsayin shugaban ma’aikatan fadar Villa.

Gambari, tsohon ministan harkokin kasashen waje a 1984-1985, kuma dan asalin garin Ilorin jahar Kwara zai maye gurbin marigayi Abba Kyari, kamar yadda sakataren gwamnati ya sanar.

KU KARANTA: Wasu dabi’u na Ibrahim Gambari da suka burge Buhari har ya nada shi shugaban ma’aikatan Villa

Cikin wata sanarwa da Tinubu ya fitar ya yaba da nadin Gambari, ina yace a matsayinsa na Farfesa a kimiyyar siyasa ya dace da wannan mukami mai matukar muhimmanci.

“Nadin da aka yi ma Farfesa Ibrahim Gambari a matsayin sabon shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa abin a yaba ne, Farfesa Gambari sanannen dan diflomasiyya ne, shahararren Malami, kuma mutum mai daraja wanda ya yi ma kasar nan bauta a matakai daban daban.

“Basirarsa, gogewarsa da kuma gwanintarsa a sha’anin mulki da diflomasiyya ya shirya shi kwarai don tafiya da irin wannan muhimmin aiki. Na taya Farfesa Gambari murna, kuma na yaba ma shugaba Buhari da daukan wannan mutumi aiki a irin wannan lokaci.” Inji shi.

Tinubu ya yi tsokaci game da nadin da Buhari ya yi ma Ibrahim Gambari
Tinubu Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Tinubu ya kara da cewa Gambari zai taimaka ma shugaba Buhari wajen gudanar da tsare tsaren gwamnatinsa kamar yadda ya yi a baya lokacin da ya yi masa minista a shekarar 1984.

“Iya sanin da na Gambari, mutum ne dake da kwarewa a fannoni daban daban wanda ya san Najeriya ciki da waje, kuma yake kaunar Najeriya, kuma yana da yakini game da burin shugaban kasa Buhari na kawo canji a kasar. Ba bako ne ga jam’iyyar APC, da manufofinta.” Inji shi.

Sai dai daga karshe Tinubu ya shaida ma Gambari cewa wannan aiki da aka bashi a wannan karo aiki ne mai wahala, wata kila ma ya fi duk ayyukan da ya taba yi wahala.

“Amma mutum ne na musamman dake da kwarewa, ina fatan zai shawo kan kalubalen yadda ya kamata ta hanyar gudanar da aikinsa da kyau.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel