Akwai yiwuwar har abada duniya ba za ta rabu da coronavirus ba - WHO

Akwai yiwuwar har abada duniya ba za ta rabu da coronavirus ba - WHO

Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta ce akwai yiwuwar kwayar cutar (COVID-19) ba zai taba tafiya baki daya ba.

Mike Ryan, babban direktan sashin bayar da taimakon gaggawa ta Hukumar Lafiya ta Duniya, ya ce akwai yiwuwar kwayar cutar coronavirus ba za ta bace a duniya ba.

Ya ce akwai yiwuwar za ta zama kamar wasu kwayoyin cuta ne da ke kashe mutane a duk shekara.

Akwai yiwuwar har abada duniya ba za ta rabu da coronavirus ba - WHO

Akwai yiwuwar har abada duniya ba za ta rabu da coronavirus ba - WHO. Hoto daga The Cable
Source: Twitter

"Akwai yiwuwar kwayar cutar kawai za ta zama kamar yadda wasu cututtuka ne da ke zuwa a duk shekara a wani yanayi suna kisa. Har yanzu bamu rabu da kwayar cutar HIV ba," Ryan ya ce a ranar Laraba.

DUBA WANNAN: Buhari ya nada sabon shugaban NALDA

"Ba kwatanta cututtukan biyu na ke yi ba amma ina ganin yana da muhimmanci mu fuskanci gaskiyar lamarin. Ba na tsammanin akwai wanda zai iya hasashen cewa kwayar cutar za ta tafi ko ba za ta tafi ba."

An fara gano HIV/AIDS ne a asibitoci a shekarar 1981 a kasar Amurka. Cutar ta kashe kimanin mutane miliyan daya kuma ta harbi mutane fiye da miliyan 38 a kasashen duniya.

Fiye da shekaru 30 da bullar cutar, har yanzu ba a gano rigakafin ta ba amma ana cigaba da bincike domin gano rigakafin saboda a ci galaba a kanta.

Ryan ya ce idan mun samu rigakafi, "Akwai yiwuwar za mu iya kawar da cutar a bayan kasa amma dai sai an samu rigakafin. Dole ya kasance mai inganci sosai kuma ya zama yana da saukin farashi da kowa zai iya samu.

"Akwai yiwuwar wannan cutar ba yanzu bane za a iya kawar da shi ko kuma akasin hakan."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel