Ranaku 10 na karshen Ramadan: JNI ta nemi al'umma su dukufa da addu'o'i

Ranaku 10 na karshen Ramadan: JNI ta nemi al'umma su dukufa da addu'o'i

Kungiyar Jama'atu Nasril Islam (JNI), ta yi kira ga Musulmai da su dukufa da addu'a a cikin kwanaki goma na karshen watan Ramadana mai alfarma.

Sakataren kungiyar, Dr Khalid Aliyu, ya yi wannan kiran ne a wata takarda da ya fitar a ranar Laraba a garin Kaduna, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta wallafa.

Aliyu ya ce,a tsaka da annobar Coronavirus, al'ummar Musulmi sun fara azumin watan Ramadan a Najeriya cike da hadin kai.

Kamar yadda yace,"Muna shirin kammala azumin mu kuma mun zo kashi mafi falala na watan.

"Mun fara neman daren laylatul Qadr wanda ake nema a ranakun 21, 23, 25, 27 da 29 na watan nan.

"A don haka, JNI karkashin shugabancin mai girma Sarkin Musulmi na yin amfani da wannan damar wajen rokon Allah da ya karba ibadunmu.

"Muna fatan ya kara mana imani kuma ya yaye wa duniya wannan annobar. Kasar mu tana cikin matsanancin hali bayan bullar cutar nan.

"Duk da kalubalen da ke kunshe da dokar takaita zirga-zirga, mun fuskanci raguwar yaduwar cutar. Muna hakuri, juriya da kuma bauta ga Allah mai duka a yayin watan nan."

Ya kara da cewa, akwai bukatar mu roki yafiya da rahamar Allah a cikin wannan watan mai alfarma.

Ranakun 10 na karshen Ramadan: JNI ta yi kira a kan tsananta addu'a
Ranakun 10 na karshen Ramadan: JNI ta yi kira a kan tsananta addu'a. Hoto daga jaridar Daily Nigerian
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Katsina: Sarkin Daura, Umar Faruk, ya warke sarai

Aliyu ya yi kira ga Musulmin Najeriya da su yi amfani da kwanaki goman karshen watan nan wajen karanta Qur'ani.

"Abu mafi muhimmanci shine mu nemi daren kaddara wanda yake zuwa a cikin daya daga cikin darare biyar kamar yadda sahihin hadisi daga Annabi ya bayyana.

"Mu yi amfani da wannan lokacin wajen fahimtar Qur'ani tare da karanta shi," sakataren yace.

Kamar yadda sakataren ya bayyana, yin salloli biyar a jam'i da taraweehi duk a hakura da su. A yi bauta a cikin gida har sai lokacin da hukumomi suka tabbatar da tafiyar annobar.

"Hakazalika, mu yi wa mamatanmu da suka rasu sakamakon wannan annobar addu'a.

"A yayin da mutane masu tarin yawa ke mutuwa kullum, wasu na ta ke dokar masana kiwon lafiya tare da yin taurin kai," yace.

Ya yi kira ga gwamnati da ta kirkiri lokacin wayar wa jama'a kai ta hanyar nuna musu hadarin da ke tattare da cutar.

Aliyu ya yi kira ga Musulmi da su ninka kyautatawar su ga jama'a ta hanyar bada sadaka ga mabukata da kuma marayu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel