COVID-19: Dan jarida ya kamu, ya harbi matarsa a Kano

COVID-19: Dan jarida ya kamu, ya harbi matarsa a Kano

Wani dan jarida mai suna Nasir Ibrahim da ke aiki da gidan talabijin na Abubakar Rimi a Kano ya tabbatar da kamuwar sa da cutar coronavirus tare da matar sa.

Nasir Ibrahim ya sanar da Premium Times cewa, ya fara nuna alamun cutar bayan ya yi mu'amala da tsohon hadimin marigayi Umaru Yar'adua, Rabiu Musa a Kano.

Premium Times ta ruwaito cewa, tsohon hadimin marigayi Yar'adua ya rasu bayan nuna alamun cutar a yayin da yake jiran sakamakon gwajin sa. Daga baya an tabbatar da cewa cutar ce ta kashe sa.

Musa ya kasance tsohon sakataren yada labarai na Yar'adua a lokacin da yake gwamnan jihar Katsina.

Kafin rasuwar sa, yana aiki a matsayin shugaban fannin sadarwa na UNICEF a jihar Kano.

Ibrahim da kan shi ya mika kan shi gwajin cutar bayan ya zargi cewa akwai yuwuwar yana dauke da cutar bayan rasuwar tsohon hadimin marigayi shugaban kasar.

A ranar Talata, Ibrahim ya sanar da abokan aikinsa cewa shi da matar sa na dauke da muguwar cutar.

COVID-19: Dan jarida ya kamu, ya harbi matarsa a Kano

COVID-19: Dan jarida ya kamu, ya harbi matarsa a Kano. Hoto daga SaharaReporters
Source: UGC

DUBA WANNAN: Katsina: Sarkin Daura, Umar Faruk, ya warke sarai

"Ina sanar da ku cewa sakamako ya nuna ina dauke da cutar korona tare da mata fa," Ibrahim yace.

Ya kara da cewa, "Na yi mu'amala da jami'in sadarwa na UNICEF a ranar 22 ga watan Afirilu. Ya rasu sakamakon cutar coronavirus a ranar 2 ga watan Mayu kuma an dauka samfur dina a ranar 6 ga watan Mayu.

"Na samu sakamakon gwajina a yau Talata, 12 ga watan Mayu wanda ya nuna ina dauke da cutar.

"Duk da babu wata alamar cutar da ta fara bayyana a tare da ni, NCDC ta shawarce ni da in killace kaina a gida. Ina auna dumin jikina, matata da yara na uku ina aike musu da shi kullum.

"Sun bukaci in sanar da su kowacce alama na ji da gaggawa. Ina bukatar addu'arku ta samun lafiya da gaggawa," Ibrahim yace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel