Sunayen mutum 12 da Buhari ya watsar yayin zaben Gambari a matsayin shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa

Sunayen mutum 12 da Buhari ya watsar yayin zaben Gambari a matsayin shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa

A yanzu duk wata tattaunawa ta kare kan wanda zai zamo sabon shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, biyo bayan nadin Farfesa Ibrahim Gambari a yau Laraba, 13 ga watan Mayun 2020.

Bayan zaman majalisar zartarwa da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta a ranar Laraba, fadarsa ta sanar da nadin Farfesa Ibrahim Gambari, a matsayin sabon shugaban ma’aikatan fadar.

Farfesa Gambari wanda tsohon ministan harkokin waje kuma tsohon wakilin Najeriya a Majalisar Dinkin Duniya, ya tsunduma aiki gada-gadan a fadar Aso Villa da ke birnin Abuja.

Rahotanni a baya bayan nan sun nuna cewa, 'yan majalisar zartarwa sun nemi a nada daya daga cikinsu a matsayin wanda zai ci gajiyar kujerar marigayi Abba Kyari.

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito a bayan, wasu daga ministocin kasar sun nemi a nada daya daga cikinsu, inda a yanzu da kaddara ta riga fata sun kwance damarar gamsar da Buhari a kan amincewa da kudirinsu.

'Yan majalisar zartarwar sun yi hangen cewa a cikinsu akwai wadanda ke da cancanta ta dora wa daga inda tsohon shugaban ma'aikatar fadar shugaban ya tsaya da aiki bayan ya kwanta dama.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, marigayi Kyari wanda ake gani a matsayin shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasar Najeriya mafi girman tasiri da kuma iko a tarihin kasar nan, ya riga mu gidan gaskiya a ranar Juma'a 17 ga watan Afrilu.

Buhari da Farfesa Ibrahim Gambari
Buhari da Farfesa Ibrahim Gambari
Asali: UGC

Ajali ya katse hanzarin Mallam Kyari a asibitin First Consultants da ke garin Ikoyin jihar Legas bayan ya sha fama da cutar korona inda ya yi jinya ta tsawon makonni.

A bisa tsari da kuma koyarwar addinin Islama, an binne gawar marigayi Kyari cikin zubar hawaye ta 'yan uwa da makusanta a ranar Asabar, 18 ga Afrilu, a makabartar dakarun soji ta Gudu da ke garin Abuja.

KARANTA KUMA: Tsohon kwamishinan Kano ya ba da labarin wahalar da ya sha yayin fama da cutar korona

Mutuwar kwararren a kan nazarin shari'a da doka wanda kuma ya shiga siyasa dumu-dumu, ta bar makeken tabo a zukatan iyalansa da dangi da kuma masoya.

Haka zalika mutuwar Kyari wanda ya kasance dan asalin jihar Borno, ta bar babban gibi a gwamnatin shugaban kasa Buhari wanda ya yi tasirin gaske a cikinta yayin jagorancinsa.

Yayin da an kai karshe kan batun wanda zai ci gajiyar kujerar marigayi Kyari, wata majiya mai karfi daga fadar shugaban kasa, ta fadi sunayen wadanda Gambari ya fito gwarzo a cikinsu.

Majiyar yayin ganawa da manema labarai ta fadi sunayen kimanin mutum 12 da Buhari yayi watsi da su yayin zaben Farfesa Gambari a matsayin shugaban ma'aikatansa.

Bajiman 'yan siyasar da Buhari ya jingine a gefe sun hadar da:

1. Ambasada Babagana Kingibe (Tsohon Ministan Harkokin waje)

2. Mallam Adamu Adamu (Ministan Ilimi)

3. Kanal Hamid Ali (Shugaban Hukumar Kwastam)

4. Boss Mustapha (Sakataren gwamnatin tarayya)

5. Mallam Nasir El-Rufa'i (Gwamnan jihar Kaduna)

6. Ya’u Shehu Darazo (Babban hadimin Buhari kan harkoki na musamman)

7. Janar Buba Marwa (Tsohon gwamnan Borno da Legas a lokacin mulkin soja)

8. Jalal Arabi (Tsohon sakataren dindindin na fadar shugaban kasa)

9. Suleiman Adamu (Ministan Ruwa)

10. Sarki Mukhtar Abba (Hadimi na musamman ga shugaban kasa Buhari)

11. Ahmed Rufa'i (Shugaban Hukumar leken asiri ta NIA)

12. Mallan Ibrahim Shekarau (Tsohon gwamnan jihar Kano)

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel