Shugaban ma’aikatan Villa: Gwamna Abdulrazak ya gode ma Buhari bisa nadin Gambari

Shugaban ma’aikatan Villa: Gwamna Abdulrazak ya gode ma Buhari bisa nadin Gambari

Gwamnan jahar Kwara, AbdulRahman AbdulRazak ya taya Farfesa Ibrahim Gambari murnar nada shi mukamin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa da shugaba Buhari ya yi masa.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito gwamnan ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da kakaakinsa, Rafiu Ajakaiye ya fitar a garin Ilorin a ranar Laraba.

KU KARANTA: Wasu dabi’u na Ibrahim Gambari da suka burge Buhari har ya nada shi shugaban ma’aikatan Villa

Gwamnan ya bayyana nadin a matsayin tabbacin sakayya ga jajircewa, aminci da kuma daddiyar alaka.

Shugaban ma’aikatan Villa: Gwamna Abdulrazak ya gode ma Buhari bisa nadin Gambari

Abdulrazak da Gambari Hoto: Daily Post
Source: UGC

“Nadin ya bayyana cewa akwai manufa a tattare da ita, kuma ya dace da dan mu, Farfesa Gambari, wanda yake da tsaftataccen tarihi a matsayin jami’in diflomasiyya da kasancewarsa babban mutum a duniya.

“A madadin iyalina, gwamnatin jahar Kwara da al’ummar jahar, ina taya Wamban Ilorin murnar samun wannan mukami. Farfesa Gambari ya dade a matsayin mutumin shugaban kasa, don haka bamu yi mamakin nadinsa mukamin shugaban ma’aikatansa a wannan lokaci ba.

“Mun yaba da karrama mu da shugaban kasa yayi, a matsayinmu na al’ummar jahar Kwara. Muna fatan Allah Ya yi masa jagora, kuma Allah Ya kare Farfesa Gambari a kan wannan muhimmin aiki.” Inji gwamnan.

Daga karshe gwamnan ya yi addu’ar Allah Ya kare shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda gwamnatinsa ke cigaba da amfanar al’ummar Najeriya.

A ranar Laraba, 13 ga watan Mayu ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanar da nadin Farfesa Ibrahim Gambari a matsayin sabon shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa.

Buhari ya nada shi ne kasantuwar shi ba dan siyasa ba ne, ga tsananin hakuri da kuma matsayinsa a duniya duba da kwarewarsa wajen mu’amalar kasa da kasa.

Haka zalika tun daga shekarar 2015 Gambari ya kasance yana baiwa shugaba Buhari shawarwari ba tare da ya taba tambayar a masa wata alfarma ba.

Gambari ya taba zama ministan harkokin kasashen waje a zamanin mulkin Buhari na Soja daga 1984-1985, don haka akwai aminci da daddiyar sanayya a tsakaninsu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel