Wasu dabi’u na Ibrahim Gambari da suka burge Buhari har ya nada shi shugaban ma’aikatan Villa

Wasu dabi’u na Ibrahim Gambari da suka burge Buhari har ya nada shi shugaban ma’aikatan Villa

A ranar Laraba, 13 ga watan Mayu ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanar da nadin Farfesa Ibrahim Gambari a matsayin sabon shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa.

Gambari dan shekara 75 zai maye gurbin marigayi Abba Kyari, wanda ya rike mukamin tun daga shekarar 2015 zuwa watan Afrilun 2020 kafin rasuwarsa daga cutar Coronavirus.

KU KARANTA: Takaitaccen tarihin Ibrahim Gambari, wanda ya maye gurbin Abba Kyari a fadar shugaban kasa

Sai jaridar The Nation ta samu wasu sahihan labaru daga fadar shugaban kasa dake bayyana dalilan da suka Buhari ya zabi Gambari daga cikin jerin mutane 14 da aka baje masa a gabansa.

Daga cikin wadannan dalilai akwai kasancewarsa ba dan siyasa ba, ga tsananin hakuri da kuma matsayinsa a duniya duba da kwarewarsa wajen mu’amalar kasa da kasa.

Wasu dabi’u na Ibrahim Gambari da suka burge Buhari har ya nada shi shugaban ma’aikatan Villa
Buhari da Gambari Hoto: Newswirelawandevent
Asali: UGC

Haka zalikar majiyar ta kara da cewa tun daga shekarar 2015 Gambari ya kasance yana baiwa shugaba Buhari shawarwari ba tare da ya taba tambayar a masa wata alfarma ba.

Idan za’a tuna, Gambari ya taba zama ministan harkokin kasashen waje a zamanin mulkin Buhari na Soja daga 1984-1985, don haka akwai aminci da daddiyar sanayya a tsakaninsu.

A wata ganawa da Buhari yayi da Gambari da safiyar Talata a Villa inda suka yi karin kumallo tare, ya bayyana masa rawar da yake bukata ya taka a matsayinsa na babban mashawarcinsa.

“Da safiyar Talata yayin karin kumallo suka gama maganansu, jim kadan bayan wannan zama sai ofisoshin jakadancin kasashen waje daka Najeriya suka bayyana farin cikinsu da nadin.” Inji majiyar.

Ga wasu daga cikin dabi’un Farfesa Ibrahim Gambari da suka burge Buhari game da shi;

- Kwarewa

- Gogewa a harkar mulki da alakar kasa da kasa

- Biyayya da aminci

- Yana da ra’ayi daya da Buhari game da tsarin ‘Next Level’

- Tsohuwar abota dake tsakaninsu

- Mutum ne mai gaskiya baya kaunar rashawa

- Ba dan siyasa bane

- Babu wasu kamiya kamiya a kansa

- Mutum ne na kowa mai zamalafiya da mutane

“Saboda haka Buhari ya zabe shi don yana son mutumin da babu ruwansa da siyasa, zai mayar da hankali ne aikinsa domin a gaggauta cimma muradun gwamnatin. Yadda aka dinga gogoriyon mukamin ya nuna yan siyasa na da manufa a kan kujerar.

“Musamman Buhari ya zabi Gambari saboda alakarsa da kasashen duniya, wanda hakan zai yi ma Najeriya amfani bayan an gama yaki da COVID-19, domin farfado da tattalin arzikin kasar tare da inganta martabar Najeriya a idon duniya.

“Koda yake akwai ministocin da ke da kusanci matuka da Buhari, amma ya kawar da kansa daga garesu, domin yin hakan zai kawo matsala ga tsarin shugabanci.” Inji majiyar.

Daga cikin mutane 14 da ake rade radin Buhari zai zaba, Gambari ne kadai ba shi da sananniyar alaka da siyasa. Da wannan nadin, Gambari ya zama mutum na 5 daya rike mukamin tun 1999.

Kuma shi ne na biyu daga jahar Kwara daya rike mukamin bayan Janar Abdullahi Mohammed 1999-2008, Mike Oghiadomhe 2010-2014, Janar Jones Arogbofa 2014-2015, Abba Kyari 2015-2020.

A zamanin mulkin marigayi Umaru Musa Yar’adua ne kadai ba’a samu wanda ya rike mukamin ba, sakamakon Yar’adua ya yi fatali da ofishin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel